KIRA GA MA’AURATA: A rika hakuri da juna, rabuwar aure ba shi da amfani – Kungiya

0

Wata Kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Moral Values and Ethics Support Foundation (MoVES)’ ta yi kira ga ma’aurata su rika hakuri da juna suna sasanta kansu domin zaman aure ya dore.

Shugaban kungiyar Pat Oseh ta fadi haka ne a tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Litini.

Pat ta ce dora wa mace nauyin gyara aure bai kamata ba domin a aure mutum biyu ne ke cikin sa wato mace da namiji.

Ta ce yanzu lokaci ne da ya kamata maza su gane cewa suna da muhimmiyyar rawar da za su taka wajen ganin an zauna lafiya a gidan aure.

Pat ta ce daya daga cikin dalilan da ya sa aure ke yawan mutuwa shine yadda maza ke nuna wa matan su iko a koda yaushe da rashin daraja su.

” awann lokaci da muke ciki na ci gaban zamani. Dole a rika baiwa mada daman nuna fasahar su da kwarewar su domin cigaba da samun zaman lafiya a gidajen auren.

Bayan haka Pat ta ce kungiyar ta shirya taro domin wayar da kan maza kan yadda za su iya gina auren su ba su rusa ta ba.

Ta ce taken taron shine ‘Dear Men’ sannan zai mai da hankali ne wajen wayar da kan maza sanin dabarun iya zaman aure tare da matayen su.

” Wani matsala kuma da yake damun kasar mu shine yadda kusan kullum taron da ake yi kan gyara auratayya mata aka fi saka wa a gaba, ba ahadawa da maza suma.

“Rashin yin haka yake sa maza na ganin matayensu a matsayin abokiyar gasar sa maimakon abokiyar zama.

Pat ta kuma ce kungiyar za ta shirya taro domin wayar da mata kan yadda za su zama shugabanni tun suna yara kanana kafin su girma.

Share.

game da Author