Khalifah Ya Cika Shekaru Sittin (60), Allah Ya Karawa Rayuwa Albarka, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah

Masha Allahu la quwwata illa billah

‘Yan uwa bayin Allah masu girma, masu daraja, muna masu sanar da ku cewa, a yau Asabar, 31/07/2021, Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II yake cika shekaru sittin (60) a rayuwarsa mai dimbin albarka, mai cike da tasiri ga al’ummar Najeriya.

Tabbas, babu shakka, rayuwar Mai Martaba wallahi, hakika, tana cike da babban darasi da dukkan wani Dan Adam, ma’abuci hankali, mai son ci gaba, kuma mai adalci, da ya kamata, kuma ya dace, yayi koyi da ita.

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

“Khairun-nasi man yanfa’un-nasa.” “Wato mafi alkhairin mutane, shine mutumin da yake amfanar mutane.”

Hakika, tabbas, ko shakka babu, rayuwar Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II, rayuwa ce da take cike da amfanar bayin Allah, kai da ma al’ummah baki daya.

Sannan Manzon Allah (SAW) yace:

“Mafi alkhairin al’ummata, shine wanda yayi tsawon rai, kuma rayuwarsa ta amfani al’ummah da dukkanin bayin Allah.”

‘Yan uwa masu albarka, lallai duk duniya ta shaida cewa, Khalifah ya kasance yana amfanar al’ummah da iliminsa, da lokacinsa, da karfinsa, kai da dukkanin abun da Allah mai girma ya hore masa.

Wallahi ‘yan uwa, duk wanda kuka ji yana suka, ko tsegumi, ko zagi, ko cin mutuncin Mai Martaba, to daya cikin biyu ne; ko a hakikanin gaskiya bai san shi ba ne, ko bai kusance shi ba. Ko kuma ya kasance ya san shi, ya kusance shi, amma tsabagen hassada, da ganin kyashi, da hikdu ba zasu bar shi ya kaunace shi ba, ko kuma yayi masa adalci.

Ni dai ina mai yi maku rantsuwa da Allah, a yau, cikin manyan mutanen kasar nan, a iya sani na, ni dai ban ga mutum mai saukin kai, irin Khalifah Muhammadu Sanusi II ba. Babu girman kai, babu raina mutane, babu wulakanci, ga son ci gaban al’ummah, ga sauraren duk wanda yazo masa da wani zance ko wani bayani!

Ina mai kiran duk wani mutum da yake adali, mai kaunar gaskiya, da cewa, don Allah, duk lokacin da kuka ji wani yana fadar maganganu na suka, zuwa ga Khalifah, to don Allah kuyi bincike, ku tabbatar, domin wannan shine umurnin Allah zuwa ga re mu, kuma shine adalci, kuma mun san da cewa, Allah yana son duk wani mai adalci.

Muna addu’a da rokon Allah ya kara wa Sarki lafiya, tsawon rai da nisan kwana. Allah ya kara wa rayuwarsa albarka. Wadannan shekaru sittin (60) da Allah ya hore masa masu albarka, ina rokon Allah ya kara masa shekaru masu dimbin albarka, masu yawa, domin wannan al’ummah taci gaba da amfana da albarkar rayuwarsa, amin.

Ina rokon Allah ya kara wa mai babban daki lafiya, da imani, da nisan kwana; Allah ya raba su lafiya, amin.

Wassalamu Alaikum,

Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author