Masu garkuwa da mutane a Jihar Katsina sun saki mutum huɗu daga cikin mutum 28 da su ka tsare, a matsayin goron Sallah ga al’ummar Ƙaramar Hukumar Batsari da ke kusa da birnin Katsina.
Mutane 28 ɗin dai sun shafe kwanaki 67 kenan a hannun ‘yan bindiga, waɗanda su ka saki mutum huɗu kaɗai daga cikin su.
Sun ce sun sake su ne matsayin ‘Barka da Sallah’ ga al’ummar yankin na Jihar Katsina, mahaifar Shugaba Muhammadu Buhari, kuma inda ya shafe mako ɗaya cur ya na hutun Babbar Sallah.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin tun a cikin watan Mayu, na yadda ‘yan bindiga su ka kashe wani attajiri, kuma su ka yi gaba da mutum 28 da shanu masu yawa a Batsari.
Amma kuma majiya daga yankin karkarar ta ce a ranar Juma’a mahara sun ce za su saki mutum huɗu, matsayin ‘Barka da Sallah’.
Sun ce za su saki wata mata da ɗan ta, bayan da mijin ta mai suna Umar Tukur ya biya su kuɗin fansa naira miliyan 2.5.
Sannan kuma wani mazaunin Batsari mai suna Misbahu Batsari, ya ce, “lokacin da za su saki Hussaina Umar, sun zaɓo wasu mutum huɗu su ka sako su tare, matsayin goron Sallah ga mutanen garin.”
Umar Batsari wanda ɗan jarida ne, ya ce waɗanda aka sako ɗin an zarce da su asibiti domin a duba lafiyar su.
Sai dai kuma ya ce waɗanda aka saki matsayin goron Sallah ɗin, duk ‘yan gida ɗaya ne. Kuma ba a san dalilin da ya sa maharan su ka saki ‘yan gida ɗaya ba.
“Kai da ganin waɗanda aka sako ɗin ka san a jigace kuma galabaice su ke. Sun ba mu labarin baƙar azabar da su ka riƙa sha a hannun ‘yan bindiga. Akwai ma wani jinjirin da aka sace tare da mahaifiyar sa, wanda ya mutu a can daji inda su ke a tsare.”
Tukur mijin Hussaina ya ƙi cewa komai dangane da lamarin, lokacin da wakilin mu ya tuntuɓe shi.
“Ni babban abin da ya shafe Ni shi ne dawowar mata ta da ɗa na, kuma sun dawo.” Haka ya shaida wa wakilin mu.
Kakakin ‘yan sandan Katsina Gambo Isa, ya shaida cewa ba shi da labarin sako mutanen shida da ‘yan bindiga su ka yi.