Kungiyar Editocin Najeriya (NGE) ta ƙi yarda da wasu sharuɗɗa da ƙorafin da Hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Talabijin ta Ƙasa ta yi, inda ta ce ‘yan jarida da gidajen biyu su na bada ƙofa ana yin kalaman da ke kawo koma-baya wajen yaƙi da ta’addanci da ‘yan bindiga.
Cikin makon jiya ne NBC ta aika wa gidajen radiyo da talabijin na faɗin ƙasar nan wasiƙu cewa a filin sharhi bayan labarai su na bayar da lokaci masu sharhi na tattauna maganganun da ke ƙara kambama ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane, har abin na haifar da koma-baya ga ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi na ganin sun daƙile matsalar tsaro.
Ba Za A Hana Mu Yin Aikin Da Dokar Ƙasa Ta Ba Mu ‘Yancin Yi Ba -Editocin Najeriya
Cikin sanarwa wadda za a iya cewa raddi ne ga Hukumar NBC, Shugaban ƙungiyar ta NGE Mustapha Isa da Sakatare Iwobosa Uwugaren sun bayyana cewa ba su yarda da furucin da NBC ta yi ba, da har hukumar ke ƙoƙarin kafa hujja da shi don ta ƙaƙaba wa kafafen yaɗa labarai da ‘yan jarida takunkumin hana su yin aikin da dokar ƙasa ta ba su ‘yancin su yi.
Sun ce hana ‘yan jarida da masu sharhi yin magana kan halin taɓarɓarewar tsaro tamkar ƙaƙaba masu takunkumi ne.
Jama’a da dama sun cika da mamakin ganin yadda a jihar Zamfara ‘yan sanda su ka bada sanarwar ceto mutum 100 daga hannun ‘yan bindiga, alhali babu wata kafar yaɗa labarai da ta bada labarin lokacin da aka sace su.
Irin wannan jama’a ke gudu idan aka ƙaƙaba wa kafafen yaɗa labarai takunkumin hana magana kan matsalar tsaro.
Farkon wannan mako ne PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin Hukumar NBC ta hana gidajen radiyo da talabijin bayyana munanan bayanan matsalar tsaro.
Hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Tashoshin Talabijin ta Ƙasa (NBC), ta bayyana cewa irin yadda ake yaɗa labarai na matsalolin tsaron ƙasar nan ya na shafar jami’an tsaron da ke kan ayyukan daƙile matsalar tsaro.
A cikin wata takardar da NBC ta raba wa gidajen radiyo da talabijin ɗin, ta ce “tabbas aika labarai da sanar wa al’mma yanayin tsaron ƙasar su abu ne da ya wajaba a kan kafafen yaɗa labarai, to kuma akwai buƙatar a riƙa isar da saƙonnin a cikin taka-tsantsan.”
Sanarwar ta ƙara da cewa waɗansu bayanan su na da nasaba da ƙabilancin da ake alaƙantawa da su, hakan na haɗa ƙiyayya, nukura, gaba da nifaƙa tsakanin ɓangarori ko ƙabilu.”
Wasiƙar dai an rubuta ta ne a ranar 7 Ga Yuli, kuma Daraktan Sa-ido kan Labarai, Francis Aiyetan ne ya sa mata hannu a madadin Babban Daraktan NBC.
NBC ta ce kafafen yaɗa labarai kada su maida hankali wajen ƙara zugugutawa ko ruruta labaran da su ka shafi mayaƙan sunƙuru, Boko Haram, ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’adda.”
Wasiƙar kuma ta umarci kafafen yaɗa labarai su daina bai wa baƙin da su ka gayyato masa yin sharhi fili su na kalaman da ke ƙara ruruta ƙiyayya tsakanin ɓangarorin ƙasar nan.
Sannan kuma ta yi kira su daina bayyana sunaye ko munin irin ɓarnar da aka yi wa jami’an tsaro, domin hakan na damun su kuma ya na taɓa tunanin su.
NBC ta runatar da su Ka’idojin Doka ta Sashe na 5.41(f) da ta 5.4.3 na Dokar NBC.
Wannan wasiƙa ta zo daidai lokacin da ake ƙorafin Gwamnatin Buhari na ƙoƙarin ƙaƙaba wa kafafen yaɗa labarai takunkumi irin wanda ya yi a lokacin da ya ke shugaba na mulkin soja.
Haka kuma ana ci gaba da nuna damuwar cewa gwamnati ta fitar da wannan wasiƙa ce ganin yadda ake yawan tsangwamar ta cewa ba ta yin abin a-zo-a-gani sosai wajen daƙile tsaro.
Discussion about this post