KANO: KAROTA ta maida lasisin tuƙa Keke NAPEP Naira 100,000 daga naira 8,000

0

Hukumar Kula da Babura da Motoci ta Jihar Kano (KAROTA), ta yi wa lasisin tuƙa A Daidaita Sahu, wato Keke NAPEP ƙarin naira 92,000.

Shugaban Hukumar KAROTA, Baffa Babba Ɗan’Agundi, ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa daga yanzu duk wanda zai yi rajistar lasisin ba shi damar tuƙa A Daidaita Sahu, sai ya biya naira 100,000 maimakon naira 8,000 kacal da ake biya kafin a yi ƙarin.

Ya sha alwashin cewa jami’an KAROTA za su fara bi kan titina su na damƙe duk wanda ba shi da lasisi da aka kama ya na tuƙa A Daidaita Sahu a Jihar Kano.

Ya ce hukumar tuni ta umarci direbobin A Daidaita Sahu su yanki lasisin tuƙi na naira 8,000, amma su ka yi kunnen-uwar-shegu da umarnin.

Tsauraran Dokokin A Daidaita Sahu A Kano:

1 – Ba a yarda a ɗauki mace da namiji tare ba (amma tuni aka yi fatali da wannan dokar, ana karya ta).

2 – Tilas da dare sai ka kunna fitila a cikin babur ɗin.

3 – Komin tsananin ruwa ko sanyi ko iska, ba yarda a ɗaura labulen hana fasinjoji jiƙewa ba.

Share.

game da Author