Kaɗan ya rage su cika mutum 1000 da suka kamu da Korona a ranakun Talata da Laraba a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta bayyana cewa a ranan Talata da Laraba mutum 939 suka kamu da Korona
Najeriya sannan mutum 5 sun rasu.

A ranan Talata mutum 404 ne suka kamu da cutar daga jihohi 12 a kasar nan.

Alkaluman sun nuna cewa mutum 356 sun kamu a jihar Legas, Rivers-18, Abuja-7, Ekiti-5, Kaduna -5, Gombe-3, Kano-3, Edo-2, Ogun-2 Beyelsa-1, Filato-1 da Nassraw-1.

A ranar Laraba mutum 535 ne suka kamu mutum, 5 sun mutu a jihohi 16 da Abuja a kasar nan.

Wannan shine karo na farko da Najeriya ta samu yawan mutane irin haka cikin watanni hudu da suka gabata.

Bisa ga alkaluman mutum 219 sun kamu a jihar Legas, Akwa-ibom-142, Oyo-47, Rivers 17, Jigawa-13, Edo-13, Ekiti-11, Bayelsa11, Ondo-10, Osun-9, Filato8, Ogun-7, Kaduna-7, Kano-5, Abuja-5, Gombe-4 da Nasarawa-3
A jimla mutum 172,263 ne suka kama cutar, mutum 2,129 sun mutu a kasar nan.

An sallami mutum 164,886 sannan mutum 5,282 na killace .

Tun bayan bullowar zazzafar nau’in cutar ‘Delta’ Najeriya ta fara samun karuwa a yaduwar korona a kasar nan.

A ranar Laraba kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta bayyana cewa nau’in ‘Delta’ ta yadu zuwa kasashe 132 sannan duk kasashen da nau’in ta bullo na samun karuwa a yawan mutanen dake kamu da cutar da yawan da cutar ke kashewa.

Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga mutane da su gaggauta yin allurar rigakafin korona.

Gwamnatin ta kuma ce ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar na cikin hanyoyin da zai taimaka wajen kare mutum da na kusa da shi kamuwa da cutar.

Share.

game da Author