Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai 26 da ƴan bindiga suka sace a Kaduna ranar Litinin

0

Kakakin Rundunar ƴan sandan Kaduna, Muhammed Jalige ya bayyana cewa jami’an ƴan sanda da na Sojojin kasa da na Sama sun ceto ɗaliban makarantan Bethel 26 da ka yi garkuwa da su da safiyar litinin.

Jalige ya ce an ceto ɗaliban ne bayan bin sawun maharan da jami’an tsaro suka yi cikin gaggawa.

Sace ɗaliban Sakandaren Bethel

A karo na huɗu cikin wata shida, ‘yan bindiga sun sake kutsawa sun kwashi ɗaliban sakandare na Bethel Secondary School da ke Marmara, cikin Karamar Hukumar Chukun ta Jihar Kaduna.

Mahara sun dira makarantar da jijjifin asubahin Litinin ɗin nan, bayan sun riƙa buɗe wuta su na harbin kan-mai-tsautsayi.

Harin ya faru ne kwana ɗaya bayan wasu mahara sun kutsa asibitin kutare na Zaria sun kwashi jarirai, nas-nas da jami’an tsaro.

‘Yan bindiga sun afka Asibitin Kutare sun kwashi jarirai, nas-nas da jami’an tsaro a Zaria.

‘Yan bindiga sun kwarara cikin Cibiyar Kula da Masu Cutar Kuturta da Tarin TB sun arce da jarirai da nas-nas da jami’an tsaro.

Sun gudu da su ne bayan sun yi musayar wuta da ƴan sanda.

Shugaban Kungiyar Kiristoci na Najeriya reshen jihar Kaduna, ya bayyana cewa cikin wadanda suka tsira daga cikin ɗaliban har da ɗan sa.

Share.

game da Author