Jami’an Kwastam sun kama wani matafiyi da kuɗaɗen kasashen waje masu yawa a filin jirgin Aminu Kano

0

A ranar Juma’a ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa reshen jihar Kano EFCC, ta bayyana cewa jami’an kwastam dake aiki a filin jirgin Aminu Kano sun kama wani matafiyi da ya taso daga kasar Saudi Arabia da kuɗin kasar Amurka har dala 184,800 da wasu kuɗaɗen kasar Saudiyya masu yawa a filin jirgin saman.

Kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren ya ce hukumar NCS ta kama Sabo Suleiman a lokacin da ya zo daukan jakar kayan sa da ya biyo jirgin saman ‘Ethiopian airline’ daga kasar Saudiyya zuwa Najeriya.

Uwujaren ya ce Suleiman ya boye kudaden ne a cikin kwalayen kunzugun jarirai wato Pampas.

Ya ce an kama Suleiman ranar 27 ga Yuni wani haɗin guiwar tsakanin jami’an Kwastam, hukumar EFCC da na SSS.

“A lissafe dai an samu dala 184,800 da kuɗin ƙasar Saudiyya wato riyal 723,310 a cikin kwalayen Pampas nannaɗe a cikin jakar matafiyin.

“A kuɗin Najeriya dala 184,800 ya kai Naira miliyan 76 sannan riyal 723,310 ya kai Naira miliyan 79 idan aka canja su.

Uwujaren ya ce hukumar NCS ta damka Suleiman ga hukumar EFCC ranar 1 ga Yuli domin ci gaba da bincike.

Shugaban hukumar NCS dake kula da shiyoyin Kano da Jigawa Suleiman Umar ya jinjina kokarin da jami’an tsaron suka yi.

Umar ya yi kira ga hukumar EFCC da ta rika bada bayanan binciken da suke yi da sauran jami’an tsaro domin samun nasaran dakile mutane masu aikata irin haka.

Share.

game da Author