IN KUNNE YA JI JIKI YA TSIRA: Duk wanda mu ka kama a zanga-zangar gogarma Sunday Igboho sai mun jijjibge shi -Shugaban ‘Yan Sandan Legas

0

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas ta bayyana cewa kada Sunday Igboho ya kuskura ko ɓatan-hanya ya kai shi Legas da sunan zanga-zanga a ranar 3 Ga Yuli.

Gogarmar neman kafa Ƙasar Yarabawa (Yoruba Nation), Sunday Igboho ya bayyana shirya zanga-zanga a Legas, ranar Asabar, 3 Ga Yuli.

Sanarwar da su Igboho su ka fitar ta ce za su yi zanga-zangar kuma babu wanda ya isa ya hana su.

“Mu na sanar da Gwamna Sanwo-Olu cewa za mu zo Legas mu yi zanga-zangar lumana. Sanwo-Olu ne ke da wuƙa da nama a Legas. Don haka shi kaɗai za mu sanar wa zuwan mu.”

Sai dai kuma Rundunar ‘Yan Sandan Legas ta ce duk mai son kan sa da arziki, kada ya kuskura ya fito zanga-zangar gogarma Igboho.

“Mu na da labarin Sunday Igboho zai shirya zanga-zanga. Shi da duk wani mai kunnen-ƙashi irin da, su sani duk wanda ya fito sai ya yaba wa aya zaƙi.”

Rundunar ta ce ta shirya tsaf domin daƙile duk wani tsagera, taƙadari ko maras jin shawarar na gaba da shi.

Dambarwsr ta zo kwana bayan wasu ‘yan bindiga sun kai mummunan hari a gidan Sunday Igboho da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Sunday Igboho dai tsohon ɗan daba kuma ɗan jagaliya ne da ‘yan siyasar ƙasar Yarabawa ke ɗauka sojan-haya domin a ci zaɓe da tsiya ko da tsimin tsiya a shekarun baya.

Ya sake sun suna wannan karo a faɗin ƙasar nan yayin da ya yi shelar korar Fulani makiyaya kakaf a jihohin Yarabawa.

Sun riƙa bi su na fatattakar Fulanin da ba su ji ba, ba su gani ba.

Share.

game da Author