Allah ya albarkaci Jihar Oyo da mata manoma, kuma hamshafai a fannin noma masu yawa. Gaga cikin su kuwa har da Olubunmi Agbato, matar da ta samu nasibi sosai a harkar kiwon kifi a jihar.
A yanzu haka ita ce Shugabar B-Spice Fish ta na sarrafa kifi zuwa kayayyaki iri daban-daban, kamar yadda za a ji daga bakin ta.
“Tun a jami’a na fara sha’awar kiwon kifi, saboda a fannin kiwon kifi na yi digiri na. Yanzu ga shi har ina kiwon kifi, ina tallatawa kuma ina sayarwa.
“Amma a gaskiya kafin na shiga jami’a, babu ruwa na da sha’awar kiwon kifi. Na so yin digiri ne kan fannin aikin likita. To daban samu ba, sai na ce Allah ya zaɓa min mafi alheri. Shi ne sai aka ba ni kwas na nazarin kiwon kifi da dangogin sa. Amma dai gaba ɗayan aikin gonar duk na karanta.
Ta ce tun da ta fara ba ta da kaico ko da-na-sani. Amma dai an sha fuskantar ƙalubale kam.
Kifayen Da Na Ke Kiwo Sun Kai 10,000:
“Ina da manyan kandamin biyu na kiwon kifi. Sannan kuma ina da matsakaitan kandami huɗu. To ka ga kandami shida gare ni. Yawan kifayen sun kai 10,000.”
An tambaye ta shin ko ita ma ta na sarrafa abin kifayen da ta ke kiwo kamar yadda wasu manyan masu kiwon kifi irin ta ke yi? Sai ta ce:
“Ban cika sayen abincin kifayen ba. Sana’ar miji na kenan haɗa abincin kifaye. Kuma ya na haɗawa da sayar da kayan kiwon kifaye. Shi ya sa abincin kifaye bai cika yi min ƙaranci ba. Amma na kan ɗan saya idan ƙananan kifaye sun kai makonni takwas.”
Ta shaida wa wakilin mu cewa ba ta daɗe da fara sana’ar kiwon kifi ba. “Na fara cikin 2017, amma dai tun cikin 2016 na fara shirye-shiryen farawa.”
Da Kuɗin ‘Alawee’ Ɗin Da Na Riƙa Tarawa Ina Bautar Ƙasa Na Fara Kiwon Kifi:
Agbato mace jajirtacciya, domin ta shaida wa wakilin mu, ta riƙa yin aikin rufa wa kai asiri a lokacin da ta ke aikin bautar ƙasa. Hakan ne ya bata damar riƙa tara kuɗaɗen alawus ɗin ta na NYSC, ba ta kashewa.
Ta ce daga cikin kuɗaɗen ne ta ɗebi Naira 100,000 ta fara jan jari da sayo wasu kayan da ta fara kiwo.
“Amma dai wani tallafi mai kauri da na samu daga wata ƙungiyar ƙasa-ƙasa ya cicciɓa sana’ar tawa har ka ga ta kai matsayin da ta ke a yanzu.”
Ta ce shi ma fa mijin ta duk lokacin da ya farauto wasu kuɗaɗe masu kauri, ya na ƙara wa sana’ar ta su ƙarfin jari.
Agbato dai mamba ce a Kungiyar Masu Kiwon Kifi ta Najeriya (FFON) kuma ta na cikin FSN.
Batun tallafi daga gwamnati kuwa, cewa ta yi ba a taɓa ba ta ko ranyo ba, saboda siyasa ta yi yawa a lamarin nema, biya da kuma ka karɓa.
Agbato ta ce ba ta da matsalar kasuwa, kuma akan samu lokacin da su ke daina kai wa masu gidajen sayar da abinci kifi ko masu yin farfesu su na sayarwa.
Shawara Ta Ga Mata Dangane Da Kiwon Kifi:
“Ina ba mata shawara cewa ba a bori da sanyin jiki. Za ki iya kiwon kifi ko da ƙaramin jari ne ɗan kaɗan. Amma ba kiwon kifi ta salon intanet a yanar gizo. Sai kin tashi tsaye. Sai kin zage damtse. Sai kin riƙa kazar-kazar. Sai kin riƙa bin diddigin komai. Ba wai ƙi shimfiɗe jiki a gida ki na kwance ba, wai ke ga oga.”
Discussion about this post