Gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya umurci jami’an tsaron jihar su kamo duk wadanda ke da hannu a rikici da kashe-kashen rayuka da ake fama da tun a watan Yuni a ƙananan hukumomin Kudancin Jos da Riyom.
Lalong ya fadi haka ne ranar Asabar a wata takarda da darektan hulda da jama’a da yada labarai na gwamnan Makut Macham ya saka wa hannu.
Lalong ya umurci jami’an tsaro da su gudanar da bincike domin gano wadanda ke tada zaune tsaye a jihar.
Gwamnan ya yi bakin cikin yadda aka kashe mutane masu ɗimbin yawa Chol da Vwang dake Kudancin Jos da Tamborong da Ganawuri dake karamar hukumar Riyom.
Ya ce rikicin da wadannan wurare suka yi fama da su ya cigaba da aukuwa ne a dalilin rashin kamawa da hukunta wanda da ke da hannu wajen ruruta wutan rikicin.
“A cikin kwanakin nan gwamnati ta kaddamar da motoci 50 da baburan hawa 200 domin inganta aiyukan jami’an tsaro a jihar.
” Muna sa ran cewa hakan zai taimaka wajen hana rikici da kama masu kokarin tada zaune tsaye a jihar. Sannan kuma za mu ga canji nan ba da daɗewa ba saboda gabaɗaya yanzu mun maida hankali ne wajen ganin zaman lafiya ta tabbata a ko’ina a faɗin kasar nan.
Lalong ya yi kira ga mutane da su taimaka wa jami’an tsaro da bayanan sirri da za su taimaka wajen damke bata gari a jihar.