A ranar Litinin ɗin nan ce Gwamnonin Jam’iyyar PDP za su yi taro a Bauchi domin tattauna batutuwa da dama da su ka shafi ƙasar nan da kuma jam’iyyar su.
Sanarwar da Babban Daraktan Ƙungiyar Gwamnonin PDP, Cyril Maduabum ya fitar, ya ce gwamnonin za su tattauna kan baturuwan da su ka haɗa da rashin aikin yi, matsin rayuwa da tattalin arziki.
Sannan za su tattauna matsayin dimokraɗiyya yanzu a Najeriya, matsalar tsaro, Ƙudirin Kwaskwsrimar Dokokin Zaɓe da Ƙudirorin Yi Wa Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa Kwaskwarima.
Har ila yau, sanarwar da Maduabum ya fitar ta ce a taron, Gwamnonin PDP za su fitar da matsaya ɗaya domin tunkarar gwamnatin tarayya kan matsalar tsaron da a kullum ke ƙara muni a faɗin ƙasar nan, tare da kawo na su shawarwari.
“Sannan kuma kowane gwamna zai gabatar da ƙalubalen da jihar sa ke fuskanta.” Inji sanarwar.
Haka kuma Gwamnonin PDP za su bijiro da tsare-tsaren sake saisaita jam’iyyar PDP, ciki har da ƙoƙarin yi wa mambobin jam’iyyar rajista ta yanar gizo.
Cikin wanan shekara dai jam’iyyar PDP ta haɗu da cikas, inda gwamnonin ta biyu su ka canja sheƙa zuwa APC mai mulki. Haka ma wasu sanatoci da aka zaɓa a ƙarƙashin tutar PDP sun koma APC.
Yayin da PDP ke fuskantar wanann ƙalubale, a kwanakin baya ta zargi ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya kai Jihar Legas cewa wani shiri ne na kaɗa gangar fara kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa na 2023 aka yi.