Gwamnonin PDP sun nemi a koma aika sakamakon zaɓe ta yanar gizo

0

Gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP, sun nemi a koma tsarin aika saƙonnin sakamakon zaɓe ta yanar gizo.

Sun nemi Majalisar Dattawa da ta Tarayya sun amince da wannan ƙudirin domin ya zama doka.

Gwamnonin sun yi wannan kiran ne a Bauchi, a taron da su ka yi ranar Litinin.

A wurin taron, sun fitar da matsayar su dangane da wasu batutuwa da ƙalubalen da ke damun ƙasar nan baki ɗaya.

Gwamnonin da suka halarta sun haɗa da Aminu Tambuwal na Sokoto, Okezie Ikoeazu na Abiya, Udom Emmanuel na Akwa Ibom, Samuel Ortom na Benuwai da kuma Ifeanyi Okowa na Delta.

Akwai kuma gwamnonin Enugu, Ribas, Oyo, Adamawa, Edo, Bauchi, Taraba da Mataimakin Gwamnan Zamfara.

Tambuwal na Sokoto ne ya karanta wa manema labarai matsayar su bayan an kammala taron.

Idan ba a manta ba, Majalisar Dattawa da ta Tarayya sun ƙi amincewa da a riƙa aikawa da sakamakon zaɓe ta yanar gizo, saboda a cewar su Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) ta shaida masu cewa rabin mazaɓun kasar nan ba su da ƙarfin intanet da zai iya aika saƙonnin ta yanar gizo.

Sai dai kuma gwamnonin PDP ce aika sakamakon zaɓe ta yanar gizo zai kawar da maguɗin zaɓe, don haka su na goyon bayan tsarin, wanda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta daɗe ta na neman a riƙa yi a ƙasar nan.

Sun kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta haɗa kai da jihohi a kawar da matsalar ɗimbin rashin aikin yi a cikin matasan ƙasar nan.

Sannan kuma gwamnonin sun yi kira gwamnatin tarayya ta gaggauta kawo ƙarshen ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Sun kuma yi kira ga ɗaukacin ‘yan Najeriya su yi amfani da damar yin rajista ta yanar gizo da INEC ta bijiro da shi, a matsayin hanyar tabbatar da sahihin zaɓe a zaɓuka masu zuwa.

Share.

game da Author