Gwamnatin Tarayya za ta fara aikin titin jirgin Kasa daga Kaduna zuwa Kano

0

Shugaba Muhammadu Buhari zai bude fara aikin titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Abuja a ranar Alhamis.

Babban Sakatare na Mai’aikatar Sufuri ta Tarayya, Magdalene Ajani ce ta bayyana haka, cikin wata sanarwar da ta fitar a ranar Talata, a Abuja.

Sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai Orjiekwe Eric, ya ce za a yi bukin ƙaddamar da fara aikin a Zawaciki, Karamar Hukumar Dawakin Kudu a Kano da ƙarfe 10 na safiyar Alhamis.

Ta ce aikin titin jirgin zai ƙarfafa shirin Shugaba Buhari na haɗa yankunan ƙasar nan da layikan dogo domin bunƙasa tattalin arziki.

Ta ƙara da cewa an gayyato masu ruwa da tsaki a harkar ayyukan da su ka shafi jiragen ƙasa domin su halarci taron.

A farkon watan Yuli ɗin nan ne PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Gwamnatin Tarayya ta bakin Ministan Sufuri ta ce ta biya dala miliyan 218, somin-taɓin fara titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano.

Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana wa manema labarai cewa Gwamnatin Tarayya ta b iya dala miliyan 218, matsayin somin-taɓin fara aikin titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano.

Amaechi ya bayyana haka yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce tantagaryar adadin kuɗaɗen kwangilar dala biliyan 1.2 ne. Amma daga cikin an fara biyan dala miliyan 218, domin a fara aikin titin cikin wannan wata na Yuli da mu ke ciki.

Amaechi ya ce yanzu hankalin gwamnatin tarayya ya karkato a kan aikin titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano, tunda an rigaya an kammala na titin Legas zuwa Ibadan.

“A yanzu abin da ya rage a biya kudin aikin su ne dala miliyan 900. Kuma nan da makonni kaɗan masu zuwa za a sake biyan dala miliyan 100.” Inji Amaechi wanda ya ce ya na sa ran zuwa ƙarshen wannan shekara za a yi ƙoƙari a biya dala miliyan 600.

Ya kuma yi magana kan sauran titinan da Gwamnatin Tarayya ta ƙudidi aniyar shimfiɗawa, kuma duk na jirgin ƙasa daga na Maiduguri da na Ibadan zuwa Kano, da na Legas zuwa Calabar.

Ya ƙara da cewa an fara biyan kuɗin somin-taɓin aikin titin jirgin ƙasa na Kano daga Kaduna daga cikin kasafin gwamnatin tarayya.

“Akwai kuma sauran kashin kuɗaɗen wanda China ce za ta biya, amma ba ta fara biyan ba tukunna.

“Kada ku tambaye ni inda Najeriya ta samu kuɗin da ta biya. Domin a matsayi na na Kirista, gidan Shaiɗan ne kaɗai ba zan iya zuwa neman bashi ba.” Inji Minista Amaechi.

Share.

game da Author