Gwamnatin Kaduna ba ta rushe gidajen Malali ba sai da ta baiwa mazauna wa’adin tashi mai tsawo – In ji Gwamnati

0

Idan ba a manta ba, mazauna gidajen gwamnati masu karamin kuɗi dake Malali, Low-Cost sun yi kwannan tsaye tun daga ranar Asabar zuwa litinin, bayan gwamnatin jihar Kaduna ta rusa wannan rukunin gidaje.

Kana dai kwance ne kawai za ka katafila na kaftun gidan ko ka shirya ko baka shirya ba.

Mutane da dama sun yi asarar dukiyoyin su.

Sai dai kuma gwamnati ta bayyana cewa sai ta ba su lokaci mai tsawo su tattara su tashi daga wannan unguwa amma mazaunan suka yi burus abin su.

Hukumar KASUPDA ta ce mutane ne suka tashi da gangar bayan sanra da su da aka yi ta yi su tashi, suka ƙi.

PREMIUM TIMES ta ci karo da wata takardar sako da wanke kanta da gwamnatin jihar ta yi kan rusa waɗannan rukunin gidaje da ta yi da sauran su.

Hukumar Raya Birane ta KASUPDA ta bayyana cewa ba haka nan kawai ta rushe gidajen Malali Low Cost ba sai da Hukumar Kula Da Kaddarorin Gwamnati ta KSDPC wanda gidajen ke karkashin kulawanta ta ba su takardar wa’adi su tashi (quit notice)

Shugaban Hukumar KASUPDA, Sama’ila Dikko ya bayyana wa manema labarai cewa wadannan gidaje, gidaje ne na gwamnati wadanda suke karkashin kulawar hukumar nan ta KDSPC kuma ta ba mutanen da suke zaune a wadannan gidajen cewa su tashi gwamnati na bukatan gidajenta. A cewar hukumar, ta ba su wa’adin sama da wata uku wanda har sai da aka rika sanya shela a gidajen rediyo amma wasu tsiraru daga cikinsu suka yi kunnen-uwan shegu.

“Gidajen Malali Lowcost gidaje ne da gwamnati ta gina domin kananan ma’aikata su zauna, yanzu an dade mafi yawan gidajen nan sun rube. In ka shiga za ka ga yadda aka yayyanka, aka yi gine-gine sai ya kasance ba magudanan ruwa wurin ya koma ba tsari ba komai. Aka mayar da wurin ya zama wurin lalata.

” Mun kira mutanen nan muka zauna da Su. Hukumar KSDPC ta kira su ta zauna da su duk abin da ya dace na uzuri an yi musu. An fada musu cewa gwamnati za ta yi amfani da gidajenta saboda asalin wadanda aka ba gidajen ba su ne ke zaune a cikin gidajen ba. Wasu ma sun bayar da gidajen haya ne ga wasu. An zauna da su ba daya ba, ba biyu ba an kuma fada musu sababbin gine-ginen da za a yi yanzu ba haya za a saka ba. In an gama siyar da su za a yi saboda haka duk  wanda ke da gida ya zo ya biya kashi goma cikin dari, sauran sai ya biya cikin shekaru biyar ko goma.

” Ina tabbatar muku duk an yi musu bayani, kuma duk an sa a gidajen rediyo ban da wannan ‘notice’ da aka ba su, sai da aka kara musu wata biyu, aka kara kara musu. Kashi tamanin din su duk sun tashi.

” Ya kamata mutane su sani, wadannan gidajen fa gidajen gwamnati ba wai nasu ba ne. Akwai wadanda suke zaune a abin da ake kira ‘carve out’ su ba a tashe su ba saboda har masu gadi muka ba su saboda kada a yi musu sata”. 

Da aka tambaye shi game da dalilin rushewar, Dikko ya bayyana cewa, ”Gwamnatin Jihar Kaduna ta rushe wadannan gidajen ne saboda sun lalace, suna bukatar a rushe su a gina na zamani. Gaba daya Malali ba kasuwa, ba wurin wasan yara da sauran abubuwa na more rayuwa. Yanzu za a gina sababbin gidaje matsakaita har da ‘yar kasuwa. Kuma kasuwar nan ba wai ta ƴan Malali ba ce kawai, hatta ƴan waje suna iya zuwa su yi siyayya”

“Ka san matsalar Malali sun fi sama da shekara aba’in ba su da kasuwa shi ya sa kake ganin a kan Liberia Road din kowa yake mayar da gidansa shago suna cin kasuwa a bakin titi”.

Sai dai kuma akwai waɗanda suke ganin taurin kan jama’a ne ke kawo musu wannan tashin hankali.

Wani mazaunin Kaduna Saminu Alfa ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa gyara wannan unguwa na da matuƙar muhimmanci.

Share.

game da Author