Gwamnan jihar Barno Babagana Zulum ya bayyana cewa gwamnati ta samu rarrar sama da naira miliyan 400 bayan tantance malamai da ma’aikatan ma’aikatar ilimi na jihar.
Zulum ya fadi haka ne a wajen taron nada kwamitin inganta ilimi da kiwon lafiya da gwamnan ya yi a garin Maiduguri.
Ya ce gwamnatin sa ta gyara kuma ta gina makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a duk fadin jihar.
A dalilin haka gwamnati ta kafa wannan kwamiti da za su taimaka wajen ganin an dauki kwararrun ma’aikata a makarantu da asibitoci sannan da tsara hanyoyin da suka dace wajen shawo kan matsalolin da ake fama da su a waɗannan fannoni.
Zulum ya ce kwamitin wanda ya kunshi mambobin majalisar dokokin jihar, shugabannin kananan hukumomi, manyan sakatarori, kodinatocin cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da sauran su za su rika ziyartan makarantu da asibitocin gwamnati dake mazabu uku a jihar domin ganin hakan ya tabbata.