‘Yan bindiga a Zamfara sun harbo jirgin yaƙin Sojojin Saman Najeriya, ɗaya daga cikin wanda ake kai masu hare-hare ta sama da su.
Rundunar Sojojin Sama ta tabbatar da harbo jirgin aka yi, amma matuƙin jirgin ya tsira da kyar.
Lamarin ya faru ranar Lahadi wajen ƙarfe 12:45 na rana, kamar yadda Kakakin Sojojin Sama, Edward Gabkwet ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar.
Yadda ‘Yan Bindiga Su Ka Harbo Jirgin Yaƙin Najeriya:
“A ranar 18 Ga Yuli, wajen ƙarfe 12.45 na rasa, Jirgin Yaƙin Najeriya samfurin Alpha Jet ya kai hari kuma ya yi nasara a dajin Zamfara. Amma a daidai lokacin da ya ke kan hanyar komawa filin saukar sa, ‘yan bindiga sun riƙa buɗe masa wuta, har su ka kakkaɓo shi, ya faɗo ƙasa a cikin jihar Zamfara.”
“An yi sa’a matuƙin jirgin ya tsira da ran sa. Kuma ya yi amfani da dabaru irin na ƙwararrun jami’an tsaro ya kuɓuta a cikin dajin.
” Matuƙin mai suna Laftanar Abayomi Dairo, ya samu nasarar ɓalle bel ɗin jikin sa daga jirgin da ya ke tuƙi.
“Sun riƙa buɗe masa masa wuta, amma ya kuɓuta kuma ya samu wata ruga aka ba shi mafaka har dare ya yi.
“Abayomi ya yi amfani da duhu ya na haska fitilar wayar sa har ya fice daga yankin da mahara ke ta neman sa, har ya kai kan sa inda sansanin sojoji su ke.”
Bayan ya kuɓuta, Abayomi ya ce dandazon maharan da su ka bi shi sun gudu ne bayan da wani jirgin da aka tura domin ya ceto shi ya riƙa shawagi kusa da inda na sa jirgin ya faɗo.
Wannan ne karo na da jirgin yaƙin Najeriya ya yi hatsari yayin kai farmaki a cikin watanni bakwai.