Gazawar Buhari ya sa na canja wa ƴa ta suna daga Buhariyya zuwa Kauthar – Yahuza Jibia

0

Ibrahim Yahuza, mazaunin ƙaramar Hukumar Jibia, ya jihar Katsina ya canja wa ƴar sa suna da ya saka mata suna Buhariyya zuwa Kauthar saboda kamar yadda yace Buhari ya gaza.

” Kwanaki shida kafin a rantsar da Buhari mata ta ta haihu. Dama kuma na yi alkawarin idan namiji ne zan raɗa masa suna Buhari, sai kuma Allah ya bani mace. Duk da haka sai na raɗa mata Buhariyya.

Sai dai Yahuza ya ce yanzu kwatakwata babu kwanar Buhari a zuciyar sa, saboda gazawar da yayi abubuwa duk sun taɓarɓare a ƙasa.

” Kowa ya san yadda na ke ƙaunar Buhari, mune yan gaba-gaba wajen nuna masa soyayya saboda muna ganin idan ya hau mulki zai kawo karshen matsalolin da ya addabe mu a kasarnan. Sai gashi maimakon haka akasi aka samu.

” Buhari bai cika alƙawuran da yayi wa ƴan Najeriya ko da guda ɗaya ne ba. Mu dai kunya ya bamu domin ya gazawa. Saboda haka na canja wa ƴa ta suna daga Buhariyya zuwa Kauthar, kuma da wannan suna zan yi mata rajistan makaranta.

Share.

game da Author