Gwamnatin Kaduna ta rufe wasu makarantu 13 da mahara za su iya afka wa a fadin jihar.
Wannan sanarwa na kunshe ne a wata takarda da shugabar kula da makarantu na jihar har Kaduna Umma Ahmed.
Umma tace gwamnati ta ba da umarnin a rufe makarantun cikin gaggawa saboda tsaro.
Ga sunayen makarantun
Faith Academy, dake titin Kachia kusa da Jakaranda; Deeper Life Academy, Maraban Rido; ECWA Secondary school, Ungwar Maje da Bethel Baptist High School, Damishi.
Sauran sun haɗa da St. Peters Minor Seminary, Katari; Prelude Secondary School, Kujama; Ibiso Secondary School, Tashar Iche; Tulip International (Boys) School and Tulip international (Girls) School.
Sannan akwai: Goodnews Secondary School, St. Augustine, Kujama, Comprehensive Development Institution (CDI), Tudun Mare da Adventist College, Kujama.
PREMIUM TIMES HAUSA ta biga labarin yadda ƴan bindiga suka afka wani makarantan Sakandare dake Damishi suka sace ɗalibai da dama a makarantan.