Kotu a jihar Kano ta umarci gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya biya mawallafin Jaridar Daily Nigerian, Ja’afar Ja’afar da kamfanin sa Penlight Media, naira 800,000 na bata masa lokaci da yayi a kotu.
Idan ba a manta ba gwamna Ganduje da kansa ya janye karar da ya shigar akan dan jarida Ja’afar Ja’afar ya tumumarsa da fidda wasu bidiyo da yayai dake nuna gwamnan yana karkacewa ya na zura bandir din daloli a aljfan jamfar sa.
An yi ta kai ruwa tsakanin Ganduje da Ja’afar wanda ya kai ga shi ja’afar din ya koma kasar birtaniya da zama kwatata-kwata.
Ja’afar ya ce ba zai dawo najeriya sai ya tabbata ya samu kariya da iyalan sa.
A zaman kotun da aka yi ranar Talata, Maishari’a Suleiman Na-mallam ya ce tunda shi da kansa Ganduje wanda ya shigar da kara ya janye karar, kotu ta yanke masa tarar naira 800,000 da zai baiwa Ja’afar da kamfanin sa PenLight.
Sai dai kuma sai da aka yi jani-in-jaka a kutu domin lauyoyi masu kare Ja’afar sun ce a dalilin bata wa wanda suke karewa lokaci da Kotu ganduje yayi, sai ya biya shi naira miliyan 800 ne.
Haka aka yi ta kai ruwa rana tsakanin lauyoyin har dai a karshe mai shari’a Suleiman Na-mallam ya bayyana cewa naira 800,000 ne gwamna Ganduje zai biya.