GABA KURA BAYA SIYAKI: Yadda manoman da Boko Haram su ka raba da gonakin su ke rayuwar ƙunci a Sansanonin Gudun Hijira a Barno

0

Amina Adam mace ce mai himmar noma a Ƙaramar Hukumar Marte, wadda bayan Boko Haram sun raba su da garin su da gonakin su, ta ke zaman gudun hijira a Sansanin Bakassi. Sai dai a yanzu ta samu wata ‘yar gona kusa da sansanin da ta ke rayuwa fiye da shekaru huɗu kenan.

Shi kuma Buba Gambo daga Konduga aka fatattake shi, ya tsallake ya bar gidan sa da gonakin sa. A yanzu buga-buga ya ke yi a Maiduguri a cikin halin ƙunci, talauci da ƙasƙanci a Maiduguri.

“Kafin na tsinci kai na a wannan halin ni manomin shinkafa ne, har mu kan noma buhu 200 na shinkafa a kowace shekara. Amma yanzu abin ya faskara, saboda tsakanin mu da gonakin mu sai dai a mafarki, amma zuwa ya gagare mu.”

Irin matsanancin halin da Gambo ke ciki, haka dubban manoma a Jihar Barno su ka tsinci kan su, bayan Boko Haram sun kassara su, sun raba su da muhallin su.

Yaƙi da Boko Haram na tsawon shekaru 12, wanda ya yi sanadiyyar kisan fiye da mutum 35,000 ya gurgunta masu rayuwar su ta yau da kullum.

Kamar yadda ya takaita su, haka ya takaita miliyoyin jama’a a Kamaru, Chadi da Nijar.

Maiduguri, babban garin da Boko Haram ya fi yi wa illa, yanzu cike ya ke maƙil da ɗimbin ‘yan gudun hijira, waɗanda su ka su ka baro gonakin su, kamar irin su Gambo.

Noma wanda shi ne sana’ar mutanen yankin Arewa maso Gabas, a yanzu ya na fuskantar babban ƙalubale, saboda zuwa gona ya gagari manoman da Boko Haram ke fakon sace su a gonakin.

Hakan ya haifar da taguwar amfanin gonar da ake nomawa. Kuma matsalar ƙarancin abinci da manoman karkara ke shukawa.

Ita kuwa Maryam Usman mai shekaru 57, ta nuna damuwa dangane da yadda ta tsallake, ta bar gona mai faɗin hekta 10 a ƙauyukan Tauri da Jajan Kalwa da ke cikin Ƙaramar Hukumar Konduga.

“Kafin Boko Haram su fatattake mu, na kan noma shinkafa da masara da wake fiye da buhunna 300 a kowace shekara.” Inji ta.

Saboda hare-haren ‘yan bindiga an rufe hanyoyi, an hana noma amfanin gona mai fitowa ya yi rsawo sosai. Sannan ga dokar hana yawan fita, taƙaita sayar da fetur, takin zamani da wasu kayayyaki masu yawa a Jihar Barno.

Irin yadda rashin tsaro ya addabi harkar noma a Jihar Barno, haka ya kassara kiwon kifi da kiwon dabbobi ko cinikin dabbobin.

Amfanin gonar da aka fi nomawa a Barno sun haɗa da gero, dawa, wake, gyaɗa, alkama, shinkafa da kuma kayan miya, irin su albasa, tumatir, yalo, karas da sauran su.

Dukkan waɗanda aka raba da gidajen su kuma dama sun dogara ne kan harkokin noma domin samun kuɗi tun kafin a raba su da gonakin su da gidajen su.

Manajan Sansanin Gudun Hijira na Daloli na 2, Mu’azu Garba ya bayyana cewa fiye da kashi 90% bisa 100% na ‘yan gudun hijirar da ke zaune a sansanin sa, duk manoma ne da Boko Haram su ka kora daga garuruwan Bama, Konduga da Gwoza.

Sansanin Dalori na 2 da ke Kofa, cikin Ƙaramar Hukumar Konduga, ya na ɗauke da mutum fiye da 16,000. An buɗe shi tun a cikin 2014.

Share.

game da Author