EL-ZAKZAKY: Zamu daukaka kara – Gwamnatin Kaduna

0

Lauyan dake ke wakiltar gwamnatin Kaduna a shari’ar El-Zakzaky ya Dari Bayero ya ce kotu a Kaduna va ta yi wa gwamnatin Jamus har adalci ba.

Bayero ya ce maishari’a Kurada bai duba ainihin korafin da gwamnatin Kaduna ta mika a gaban kotu ba, saboda haka tabbas za mu daukaka kara, ko tantama babu.

Idan ba a manta ba kotu a Kaduna ta yanke hukuncin shari’ar Elzakzaky da ake ta kai komo akai shekaru sama da biyar.

Mai shari’a Gideon Kurada ya saki Elzakzaky sannan ya wanke shi tas daga tuhumar da gwamnati ke yi masa.

Maishari’a Kurada yace gaba ɗaya laifukan da gwamnatin Kaduna ke tuhumar El-Zakzaky ya aikata ba laifuka bane da aka aikatasu kafin lokacin da aka shigar da karar.

Saboda haka ya yanke hukuncin sallamar sa, sannan ya ce ya yi tafiyar sa gida tare da matar sa.

Share.

game da Author