El-Rufai ya yi alhinin rasuwar sojoji biyu da ƴan bindiga suka kashe wajen kare ɗaliban makarantan Bethel

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi alhinin rasuwar sojoji da suka rasu wajen kare ɗaliban makarantar Bethel da mahara suka afka wa a Kaduna.

Sojojin masu suna Rabiu Mohammed da Bilal Mohammed sun rasu ne a lokacin da suke batakashi da ƴan bindiga da suka sace ɗalibai masu yawa a makarantar Sakandare na Bethel ranar litinin.

Ƴan bindiga sun yi awon gaba da ɗalibai da dama da har yanzu ba a san yawan adadin su ba a wannan makaranta a cikin dare.

A sakon jaje da ta’aziyya da gwamna El-Rufai ya aika wa iyalai da ƴan uwan mamatan, ya yi addu’ar Allah ya gafarta musu ya kuma kai rahama cikin kabururrukan su.

Sannan kuma gwamnati ta aika musu da ɗan ihsani da ga gwamnatin jihar.

Kwamishinan Harkokin Tsaron Jihar Kaduna Samuel Aruwan na daga cikin waɗanda suka halarci jana’izan waɗannan sojoji da suka sadaukar da rayukaan su.

Iyayen yaran makarantan Bethel da aka sace sun fito bakin titi sun zanga-zangar nuna rashin jin daɗin su kan abin da ya faro.

Share.

game da Author