Jam’iyyar PDP ta nemi a gaggauta gudanar da ƙaƙƙarfan bincike dangane da dangantarkar harƙalla tsakanin fitaccen ɗan damfara Raman Abbas, wato Hushpuppi da kuma Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Abba Kyari.
PDP ta yi wannan kira ne cikin wata nasarwar da Kakakin Yaɗa Labarai Kola Ologbondiyan ya fitar ranar Alhamis, a Abuja.
Kotun Amurka ce dai ta miƙa wa Hukumar Binciken Laifuka ta ƙasar, wato FBI wani bayanin sirri wanda ya nuna ƙarara Kyari na ɗaya daga cikin waɗanda aka kasafta wasu kuɗaɗen damfara aka ba shi kasafi ya karɓa.
Hushpuppi da ake tuhuma a kotun Amurka ne bayan tsawon shekara ɗaya ana tuhumar sa, ya amince cewa ya aika laifin, kuma ya lissafa har da Kyari a cikin mutum bakwai da su ka amfana da kuɗaɗen har dala miliyan 1.1 da aka damfari wani ɗan kasuwa, mutumin Qatar.
Yayin da Kyari ya fito a shafin sa na Facebook ya ƙaryata.
PDP
Jam’iyyar PDP ta ja kunnen Gwamnatin Buhari cewa kada ta sake ta yi wa wannan badaƙala riƙon-sakainar-kashi, domin matsalar fa daf ta ke da zubar wa gwamnatin Najeriya mutumci warwas.
Har ila yau PDP ta ce gwamnatin APC ta kifar da garin martabar Najeriya a cikin rairayi.
“Jam’iyyar PDP na neman mulkin APC kada ma ya kuskura ya binne wannan harƙalla da badaƙala a hankaɗen gado ko hankaɗen filo. Domin bayanai marasa daɗi na dangantakar Kyari da Hushpuppi sai ƙara bayyana su ke yi.
“Sannan kuma idan Gwamnatin Buhari ba ta ɗauki wannan batu da muhimmanci ba, to zai zubar da ƙimar ‘yan sandan Najeriya da jami’an tsaron ƙasar baki ɗaya.”
Tuni dai Sufeton ‘Yan Sanda ya umarci kafa Kwamitin Binciken Abba Kyari, bayan da Hukumar FBI ta kaɗa ƙararrawar neman sa da kuma kiran a damƙa mata shi, domin su bincike shi.