Dagacin Boku da sauran mutane sun arce, an banka wa gidaje 100 wuta a Jihar Neja

0

Aƙalla gidaje 100 aka banka wa wuta a ƙauyen Boku da ke cikin Ƙaramar Hukumar Lavun a Jihar Neja.

Lamarin ya faru ne yayin da faɗa ya rincaɓe tsakanin mazauna Boku da mazauna ƙauyen Doko, waɗanda ke ƙarƙashin ƙaramar hukuma ɗaya.

Rikicin dai PREMIUM TIMES Hausa ta gano cewa daɗaɗɗe ne, ba a wannan karo su ka fara faɗa a tsakanin su ba.

Majiyoyi da dama sun bayyana cewa, an shafe shekaru 30 ana yi wa juna kallon-hadarin-kaji, sai a ranar Laraba ce faɗan ya yi muni.

Bayan ƙona gidaje da dukiya mai tarin yawa, an kuma kashe mutum biyu a Boku, da su ka haɗa da Alkali Kolo da Ahmadu Yabata.

Kisan-gillar da aka yi masu ya yi muni, har PREMIUM TIMES Hausa baza ta iya buga hotonan mamatan ba.

An banka wa gidan babban jigon ƙauyen, mai suna Hussain Liman wuta, haka nan kuma a babbake motar sa.

Mutanen ƙauyen sun shaida wa wakilin mu cewa, bayan harin ranar Laraba, an sake kai wa ƙauyen hari a ranar Juma’a da safe, aka ƙone wasu gidajen da dama.

Mutanen garin har da Dagacin Baku, Hussain Liman sun tsere inda a yanzu haka su ke gudun hijira a wasu ƙauyuka. Waɗanda aka ji wa ciwo kuwa su na asibiti.

Salasalar Rikicin Da Ya Ƙi Ci Ya Ƙi Cinyewa:

Majiya ta shaida wa wakilin mu cewa ƙaramin faɗan na ranakun Laraba da Juma’a ya ɓarke ne bayan an sha zaman sasanta ɓangarorin biyu sau da dama.

Zaman sasantawa na ƙarshe, shi ne wanda aka yi a gaban Etsu Nupe, Yahaya Abubakar, babban Basaraken Sarakunan Neja.

Zaman wanda aka yi har da Hussain Liman, Etsu Nupe ya shawarci ɓangarorin biyu cewa su je kotu a raba masu gardama da husuma a can.

“Mutanen Kauyen Dogo sun zo har ƙauyen mu Baku su na yi mana barazana, har sau uku.

“A ranar Laraba kuma sun biyo ta ƙauyen mu kamar za su wuce su tafi gona. Amma su na zuwa bayan gari sai su ka riƙa kame mana rumakai da awakai.

“Rikici ya ɓarke lokacin da mutanen ƙauyen mu su ka fito kwantar dabbobin su.

“Daga nan sai mutanen ƙauyen Dogo su ka fito su na harbin mutanen mu da bindigogi. Sun kashe mutum biyu, sun ji wa mutane da dama raunuka.” Inji Liman.

Kakakin Yaɗa Labarai na Rundunar ‘Yan Sandan Neja, Wasiu Abiodun ya ce an tura jami’an tsaro da yawa a yankin.

Share.

game da Author