DA ƊAN GARI A KAN CI GARI: Sojoji sun damƙe mutane 17 da ake zargin su na haɗa baki da masu garkuwa a Zamfara

0

Gwamnatin Jihar Zamfara ta tabbatar da kamun da sojoji su ka yi wa mutum 17 a garin Ɗansadau, cikin Ƙaramar Hukumar Maru.

Sojojin sun riƙa bi gida-gida ne su na bincike, tare da damƙe waɗanda ake zargi ɗin da hannu wajen sanar wa masu garkuwa mutanen da su ke damƙewa.

Kakakin Yaɗa Labarai na Kakafen Soshiyal Midiya na Gwamna Bello Matawalle, Ibrahim Zauma, ya tabbatar da kame mutum 17 a garin Ɗansadau. Sai dai ya ce ba shi da wani cikakken bayani, amma dai ya san sojoji sun shiga garin sun riƙa farautar waɗanda aka ba su rahoto na sirri cewa su na haɗa baki da masu garkuwa.

Ɗan Majalisar Dokoki mai wakiltar Ƙaramar Maru ta Kudu, Kabiru Ɗansadau, ya tabbatar da kamen da sojojin su ka yi a garin sa, Ɗansadau.

Garin dai ya na da tazarar kilomita 99 daga Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Kuma ya sha fama da ‘yan bindiga waɗanda ka riƙa kashe su su na sace masu dukiya, tare da yin garkuwa da mutane da dama.

Share.

game da Author