Akalla mutum 30 ne suka rasu a dalilin kamuwa da cutar Kwalara jihar Jigawa a watan da ya gabata.
Adadin yawan mutanen da aka samu a jihar ya kara yawan mutanen da cutar ta yi ajalinsu a kasar na.
Jihohin Enugu, Benue, Filato da Bayelsa na cikin jihohin da suka rasa mutanen su a dalilin wannan cuta a cikin makon da ya gabata.
Babban sakataren ma’aikatar kiwon lafiyar jihar Jigawa Salisu Mu’azu ya ce mutum 30 din da suka mutu na daga cikin mutum sama da 2,000 da suka kamu da cutar a kananan hukumomi 9 dake jihar.
Kananan hukumomin Hadejia da Dutse na daga cikin kanana hukumomin da suka fi fama da yaduwar cutar.
Mu’azu ya ce cutar ta barke ne a dalilin yawan yin bahaya a waje da ake yi a jihar.
“A karamar hukumar Hadejia akwai wata makarantar Almajirai da suke yin bahaya a waje wanda inda ruwan sama ya zo sai ya wanke dattin bahayan zuwa rafin da mutane ke diban ruwa su sha su girka abinci da shi.
Ya ce gwamnati ta hana amfani da ruwan wannan rafi har sai ta kammala gudanar da binciken ta.
Mu’azu ya ce idan aka yi bahaya a waje ruwan sama na wanko kazantar zuwa cikin rijiyoyi da rafi da mutane ke amfani da su wajen girki ko sha.
Ya ce gwamnati ta bada umurnin bada maganin cutar kyauta wa duk wanda ya kamu da cutar jihar.
Hanyoyin gujewa kamuwa da cutar
1. Tsaftace muhalli.
2. Wanke hannu da zaran an yi amfani da ban daki.
3. A guji yin bahaya a waje.
4. Amfani da tsaftattacen ruwa.
5. Wanke hannu kafin da bayan an ci abinci.
6. Cin abincin dake inganta garkuwan jiki.
7. Yin allurar rigakafi
8. Zuwa asibiti da zaran an kamu da cutar.
likitoci sun yi kira da arika gaggauta garzaya asibiti domin warkar da cutar.
Discussion about this post