Bayan tashi daga wasan ƙarshe na Kofin Copa America wanda Ajentina ta lashe Brazil da ci 1-0, Lionel Messi ya je wurin Angel Di Maria wanda ya ci ƙwallon ya yi masa Godiya ta musamman.
Godiyar dai ta biyo bayan gorin da ake wa Messi cewa bai taɓa ciwo wa ƙasar sa Ajentina wani babban kofi ba, sai a ranar.
Ita ma Ajentina rabon da ta ci wani babban kofi tun 1993, inda ta lashe Copa America.
Bayan tashi daga ƙwallon, gaba ɗayan ƴan wasan Ajentina sun sheƙa a guje sun kewaye Messi, su na taya shi murnar fita kunyar da ya yi, tunda ya lashe kofi a lokacin da ya kusa yin ritaya daga wasa.
Maria Ya Sa Neymar da Messi Kuka:
Yayin da Messi ya kira matar sa ta ‘bidiyo kol’ ya na kukan murnar lashe kofi, shi kuwa ɗan wasan Brazil Neymar kukan rashin nasara ya riƙa yi, har sai da Messi ya ƙanƙame shi tsawon daƙiƙa 30 ya na rarrashin sa.
Ɗan bayan Brazil Thiago Silva, ya ce an yi nasara kan Brazil har cikin gidan su, a katafaren filin Maracana da ke Rio De Janeiro saboda ƴan wasan Ajentina sun hana su lailaya ƙwallo yadda su ke so.
A yanzu dai Messi ya wuce gorin da ake yi masa cewa bai taɓa ci wa ƙasar sa wani babban kofi a duniya ko a yankin Amurka ba.
Discussion about this post