CIKA AIKI: Wasu da su ka riƙa yi min mummunar addu’a da ina rusau a Abuja, tuni sun riga ni isa lahira – El-Rufai

0

Biyo bayan rusau ɗin Gwamnatin Nasiru El-Rufai ta yi a ranar Lahadi a Malali, wanda ya ɗauki hankulan jama’a, an wayi gari an tashi ana sukar gwamnan tare da caccakar sa a Arewacin ƙasar nan.

A soshiyal midiya da bankunan jama’a, a gari-gari ana zagin sa tare da masu ɗora masa munanan addu’o’i. Wasu kuma da abin ya shafa kai tsaye, su na yi masa “Allah ya isa.”

Wannan ya sa PREMIUM TIMES HAUSA ta sake kawo maku wani bayani da El-Rufai ya taɓa yi dangane da rusau ɗin da ya ke yi a Kaduna.

“Ni ba za a bude min ido ko wata barazana da addini ba. Gaskiyar ka kawai ka kawo min takardar shaidar mallakar fili da lasisin yarda ka yi irin ginin da ka yi. Shikenan fa an gama.

“A Abuja ma na rusa masallatai, na rusa coci-coci. Babu irin mummunar addu’ar da ba a yi min ba. Amma har yau ga ni da raina garau. Wasu da su ka riƙa sheƙa min ruwan mugayen addu’o’in ma su tuni sun riga ni sheƙawa lahira.”

Hukumar KASUPDA ta bayyana cewa sai da aikaa wa mazauna unguwar Malali Low-Cost su tashi tun da wuri cewa gwamnati za ta rusa wannan wuri amma suka ki tashi.

Ismail Dikko ya ce har zama sun yi za wasu daga cikin jagororin mutanen unguwan amma aka suka ki tashi har ranar rusau ya iske su.

Share.

game da Author