BIDIYON DALOLI: Ganduje ya shigar da sabuwar ƙara a Abuja

0

A wani abu mai kama da ƙi-faɗi, Gwamna Abdullahi Ganduje ya sake shigar da Jaafar Jaafar da Daily Nigerian ƙara a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, bayan da ya janye ƙarar da ya maka su a Babbar Kotun Kano.

Bayan ya janye ƙarar cikin watan Yuni, kotu ta ci Ganduje tarar naira 800,000 da aka umarce shi ya biya Jaafar Jaafar, saboda ɓata masa suna da ya yi.

Rikicin dai ya samo asali bayan da Jaafar Jaafar da jaridar sa Daily Nigerian su ka fallasa wani bidiyo da aka riƙa nuno Ganduje na karɓar rashawada cin hancin maƙudan daloli ya na dannawa cikin aljifan rigar sa.

Sammacen da ya zo hannun PREMIUM TIMES dai ya nuna cewa an bai wa Jaafar Jaafar kwanaki 14 ya bayyana gaban kotu domin ya kare kan sa.

An rubuta sammacin a ranar 15 Ga Yuli, 2021.

A ƙarar farko dai Ganduje ya shigar a Kano ya na neman Jaafar ya biya shi naira biliyan uku diyyar ɓata masa suna da ya ce an yi, domin bidiyon a cewar Ganduje ƙarya ce aka ƙirƙira, bai saci kuɗaɗen ba.

Share.

game da Author