Karamin ministan kiwon lafiya Olorunnimbe Mamora ya bayyana cewa samar da isassun dabarun bada tazarar haihuwa zai taimaka wajen rage akalla kashi 30% na mace-macen mata a lokacin da suka zo haihuwa.
Wannan alkaluma na kunshe a jawabin da ministan yayi a wajen taron tattauna hanyoyin samar da isassun dabarun bada tazarar haihuwa a kasar nan da aka yi a makon jiya.
Ya ce bincike ya nuna cewa Najeriya na cikin kasashen duniyan da suka fi samun yawan mace-macen mata wajen haihuwa.
“Bincike ya nuna cewa mata 512 daga cikin mata 1,000 na mutuwa wajen haihuwa a Najeriya.
Matsaloli
Mamora ya ce rashin ware isassun kudade domin samar da dabarun bada tazarar haihuwa na daga cikin matsalolin da ake fama da su a kasar nan.
Ya ce sauran matsalolin sun hada da rashin sani, camfi da yadda wasu mazan basu yadda mace ta bada tazarar haihuwa.
Wayar da kan mutane
Kodinatan shirye-shirye na kungiyar RMCH Emmanuel Lufadeju ya ce sakamakon bincike ya nuna cewa akalla mata kashi 80% basu da ilimin amfani da dabarun bada tazarar haihuwa.
A Najeriya mata kashi 15% ne ke amfani da dabarun.