Jam’iyyar APC ta ƙaryata zargin da PDP ke yi cewa akwai akwai tuggun da ta ke shiyawa domin Shugaba Muhammadu Buhari ya gaji kan sa, wato ya yi tazarce bayan ya kammala wa’adin zangon sa na biyu a 2023.
Sakataren APC na Riƙo na Ƙasa, John Akpoboghedode ne ya bayyana haka, inda ya ce PDP gwano ce, ba ta jin warin jikin ta.
Sakataren ya ce APC na tafiyar da harkokin ta a tsanake ne har a yi taron gangamin jam’iyya na ƙasa, inda za ta fitar da ɗan takarar da jam’iyyar za ta cimma matsaya guda ɗaya kan amince duk a mara masa baya.
Ya ce PDP gani ta ke yi saboda ta ƙirƙiro tsiya da shegantakar tazarge-zango-na-uku wanda bai yi nasara ba, to gani ta ke yi kowace jam’iyya mai mulki ma za a iya yin irin abin da PDP ɗin ta yi.
Idan ba a manta ba, jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa APC mai mulki na ƙulla tuggun siyasar da za a bai wa Shugaba Buhari hurumin zarcewa kan mulki, bayan kammala wa’adin sa na biyu kuma na ƙarshe a cikin 2023.
Wannan batu ya taso ne a daidai lokacin da Kakakin Shugaba Buhari ya furta cewa babu wata jam’iyya mai ƙarfin iya ƙwace mulki daga hannun APC a zaɓen 2023.
Garba Shehu ya yi wannan furuci ne a Daura, Jihar Katsina inda ya je hutun Sallah tare da Shugaba Buhari.
Shehu ya ce PDP mafarki kawai ta ke yi, amma ko kaɗan ba ta da ƙarfin iya yin kokawar ƙwace mulki a hannun APC a 2023.
“Shugaba Buhari na da ɗimbin masoya a kasar nan. Don haka mun san ba za su sake shi su kama ƙafar-wala a zaɓen 2023 ba.
“Duk da matsalar tsaro ko koma-bayan harkar tsaron da ake ta ƙoƙarin a kawar da ita a ƙasar nan, hakan ba zai hana ɗimbin masoya Buhari ba za su ƙi zaɓen wanda Buhari ya nuna shi ne zai ci gaba da ɗabbaƙa ayyukan raya ƙasar da ya yi wa al’ummar kowane yanki a faɗin Najeriya ba.”