BA CINYA BA, ƘAFAR BAYA: Ban karɓi cin hanci daga ɗan damfara Hushpuppi ba, na dai haɗa shi da tela – Abba Kyari

0

A bisa dukkan alamu dai reshe na neman juyawa da mujiya ko kuma a ce ‘na shiga ban ɗauka ba, ba ta fidda ɓarawo’ kan dangantakar riƙaƙƙen ɗan damfara Abbas Raman da a faɗin duniyar nan aka sani da Hushpuppi da kuma jarumin Ɗansanda Abba Kyari.

Hushpuppi da ke tsare a hannun jami’an tsaron Amurka tun cikin watan Yuni, 2020, ya yi iƙirari a bayanin da ya yi masu cewa ya bai wa Kyari kuɗi ya kama abokin haƙallar sa, dangane da saɓanin da ya shiga tsakanin su, wurin raba wasu kuɗi dala miliyan ɗaya da su ka damfari wani Balarabe a Qatar.

Sai dai kuma da ya ke ƙaryata zargin, Abba Kyari ya ce ƙarya ne, ba haka zancen ya ke ba.

Ya ce Hushpuppi dai ya ga hotunan shi Kyari ɗin a shafin sa na Facebook, ya na sanye da kayan gargajiya har ya yi sha’awa.

Ya kira Kyari ya ce ya na son irin su. Kyari ya ce ya haɗa shi da telan sa ya tura wa telan kuɗi naira 300,000 ya ɗinka masa kayan kuma ya saya masa huluna.

Kyari ya ce bayan an ɗinka kayan da hulunan, telan ya kai kayan ofishin sa.

Yadda Na Haɗu Da Hushpuppi Har Na Yi Masa Dillancin Riguna Da Huluna -Abba Kyari

“Abbas wanda daga baya mu ka gano ana kiran sa Hushpuppi, ya kira ofishin mu kamar shekaru biyu da su ka gabata. Ya yi ƙorafin cewa wani a nan Najeriya ya yi barazanar zai kashe shi da iyalan sa a nan Najeriya. Kuma ya aiko mana lambar wayar mutumin, ya roƙi mu gaggauta ɗaukar mataki tun kafin ya kai ga kashe iyalan na sa.

“Mun je mun gano inda wanda ake zargin ya ke, mu ka yi bincike kuma mu ka gano gaskiyar magana babu wata barazanar kisa a lamarin. Ashe ma abokan juna ne tsawon shekaru masu yawa. Kawai dai saɓani ne ya shiga tsakanin su a kan kuɗi. Daga nan mu ka saki wanda ake zargin a kan beli. Ko kulle shi ma ba a ba.

“Babu wanda ya nemi ko sisi a hannun Hushpuppi. Mu a lokacin babban aikin mu shi ne mu hana wanda aka ce zai yi kisa aikata abin da aka ce mana zai aikata ɗin.

“To daga nan sai ya ga wasu hotuna da na ke sanye da kayan gargajiya a shafi na na soshiyal midiya. Ya ce ya na buƙata. Na haɗa shi da tela na, ya aika wa telan N300,000 a asusun telan na banki. Aka ɗinka masa kaya da kuma huluna biyar. Daga nan ya aiko wani ya karɓar masa a ofishin mu.

“Don haka masu ƙoƙarin ɓata mana suna har su na cewa mun karɓi maƙudan kuɗaɗe a hannun Hushpuppi, za su ji kunya. Domin ba mu tsoma hannun mu cikin dagwalon kuɗaɗen harƙalla ba, kamar yadda wasu ke watsawa.” Inji Kyari.

Share.

game da Author