Gwamnatin Tarayya ta ɗauki ma’aikata 159 tare da ba su horo don sa ido kan ayyukan Shirin Haɓaka Rayuwa, wato ‘National Social Investment Programmes’ (NSIP) a jihohin Kebbi da Ondo.
A yayin da aka ɗauki mutum 70 a Kebbi, a Ondo an ɗauki mutum 89.
Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta bayyana haka a wajen tarurrukan raba takardun kama aiki da na’urorin aikin ga ma’aikata masu zaman kan su da aka horas waɗanda aka yi a Birnin Kebbi da kuma garin Akure.
A taron Birnin Kebbi, ministar ta bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ne ya ƙirƙiro shirin na NSIP a cikin 2016 da nufin ceto jama’a daga ƙangin fatara ta hanyar wasu tsare-tsare da su ka haɗa da shirin nan na samar da aikin yi, wato N-Power, da Shirin Ciyar da Yara ‘Yan Makaranta Daga Gida (National Home-Grown School Feeding Programme, NHGSFP), da shirin Tura Tsabar Kuɗi (Conditional Cash Transfer Programme, CCT), da kuma Shirin Samar da Sana’a da Ƙarfafawa na Gwamnati (Government Enterprise and Empowerment Programme, GEEP).
Ta ce an ɗauko waɗannan shirye-shiryen aka mayar da su Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya a cikin 2019 bayan an ƙirƙiro ma’aikatar.
Sadiya ta ƙara da cewa ana aiwatar da waɗannan shirye-shiryen a jihohi 36 na ƙasar nan da kuma Gundumar Babban Birnin Tarayya.
Ministar, wadda ta samu wakilcin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Al’amuran Shari’a, Aminu Shamaki, ta ce ana sa ran cewa kowane ma’aikaci mai sanya ido zai kula da wasu keɓantattun mutanen da su ka amfana da shirin na NSIP.
Za a biya ko wannen su N30,000 a duk wata.
Ta ƙara da cewa tilas ne su cimma nasarar aƙalla kashi 80 cikin ɗari na sakamakon aikin da ake so su samu kafin su cancanci a biya su.
Ministar ta ƙara da cewa, “Takardun kama aiki na ma’aikatan sa ido ɗin su na ƙunshe da bayanan inda mutum zai yi aiki a ƙarƙashin shirin na NSIP a ƙaramar hukumar mulki da aka ba shi, kuma ya kawo rahoto mai ɗauke da shaidu kan abubuwan da ya gano a lokacin gudanar da aikin sa bisa ga bada rahotannin da aka tsara kamar yadda aka gindaya masa tare da halartar dukkan tarurrukan bita, kamar yadda dokar ma’aikatar ta ce, da sauran ayyukan da za a iya ba shi.”
Haka kuma ta yi gargaɗin cewa ba a yarda wani ma’aikaci ɗan aikin sa ido da aka ɗauka ya ba wani daban aikin ya yi ba.
Ma’aikatar za ta kama mutum idan ya aikata laifi dangane da aikin da aka ɗauke shi.
“Ina kira a gare ku da ku aiwatar da wannan aiki da gasken gaske, da tsare gaskiya,” inji ta.
A nasa jawabin, Darakta-Janar na Hukumar Sauya Tunani ta Ƙasa (NOA), Dakta Garba Abari, ya bada tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya ta kashe maƙudan kuɗi wajen yaƙi da yunwa da fatara a dukkan jihohi 36 na ƙasar nan da kuma Gundumar Babban Birnin Tarayya.
Abari, wanda ya samu wakilcin Daraktan NOA na Jihar Kebbi, Joseph Yaro-Mackika, ya yi kira ga ma’aikatan sa idon da su yi aiki tuƙuru wajen sauke nauyin da aka ɗora uku.
Ya ƙara da gargaɗin su da kada su kuskura su aikata wani laifi kowanne iri ne. Ya ƙara da cewa a yayin da su ke aikin su na kuma tunawa da cewa ita ma NOA za ta sa ido a kai tare da shawartar su don saisaita ayyukan su.
A taron Akure kuma, wanda aka yi a ranar 5 ga Yuli, 2021, Hajiya Sadiya ta ce Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta ɗauki mutum
89 tare da ba su horo da kayan aiki don sa ido kan ayyukan ta na shirin NSIP a Jihar Ondo.
Ta ce su ma za a riƙa biyan kowannen su alawus ɗin N30,000 a wata.
A wannan taron ma, ta faɗa masu manufar shirin da yadda aka horas da ma’aikatan.
Ministar dai ta samu wakilcin wata Mataimakiyar Darakta a ma’aikatar ne, Hajiya Jumai Ali.
Ministar ta ce, “Ina kira a gare ku da ku aiwatar da wannan aiki cikin kishin ƙasa sosai da kuma ƙwazo da tsare gaskiya. Mu a Ma’aikata ba za mu amince da aikin da ya saɓa wa tsarin da aka kafa ba.”
A jawabin ta a taron, Babbar Mashawarciya kan Hulɗa da Hukumomi ga Gwamna kuma jami’a mai kula da Shirin Haɓaka Rayuwa ta Jihar Ondo, Hon. (Mrs.) Bunmi Ademosu, ta yi kira ga ma’aikatan sanya ido ɗin da su maida hankali ga ayyukan su domin an dogara sosai gare su.
Ta ƙara da cewa tasirin su ya na da muhimmanci wajen cimma nasarar shirin.
Ademosu ta yi amfani da wannan damar ta bayyana sadaukarwar gwamnatin jihar ga tallafa wa talakawa da faƙirai ta hanyar shirin na N-SIP.
Ta yi kira ga ma’aikatan sa idon da su taimaka wajen sauya fasalin tarihin Nijeriya, sannan a matsayin su na matasa lallai ne su shiga cikin yaƙi da fatara da cin hanci a ƙasar nan.
Ta nuna cewa an saka manhajar Shirin Haɓaka Rayuwa a cikin ƙananan komfutocin ‘tablet’ da aka rarraba masu, tare da bayyana cewa idan an yi amfani da manhajar yadda ya kamata, za a cimma babbar nasara a aikin.