AREWA A HANNUN ‘YAN BINDIGA: Yadda masu garkuwa da ɗaliban Islamiyyar Tegina su ka riƙe mai kai kuɗin fansa, bisa zargin kuɗin ba su cika ba

0

‘Yan bindigar da su ka sace ɗaliban Islamiyyar Salihu Tanko a Tegina da ke Ƙaramar Hukumar Rafi a Jihar Neja, sun riƙe dattijon da aka aika kai kuɗin fansa naira miliyan 30, bisa zargin cewa kuɗin ba su cika cif-cif ba.

Tun farko dai iyayen yaran ne su ka haɗa naira miliyan 25, kamar yadda Shugaban Makarantar Salihu Tanko, mai suna Abubakar Alhassan ya shaida wa Sashen Hausa na BBC a ranar Lahadi cewa ‘yan bindiga sun riƙe Ƙasimu Barangana, ɗaya daga cikin mutum bakwai da aka aika su kai kuɗin fansar.

Lokacin da ‘yan bindiga su ka ƙirga cikon naira miliyan 30, sai su ka samu babu naira miliyan 4 da naira 600,000 kenan.

Alhassan ya shaida wa BBC cewa wasu iyayen duk sun sayar da gonakin su ne, wasu muhallin su, kai har wani ɓangare na makarantar aka sayar, don dai a haɗa kuɗin fansar ɗaliban Islamiyyar.

Ya ce a haka da karo-karo aka haɗa naira miliyan 30 da kyar. Sai su ka tura Barangana da wasu mutum shida domin su kai kuɗin.

Kamar yadda Alhassan ya bayyana, bayan an kai kuɗin, sai ‘yan bindigar su ka tafi da Barangana can wani wuri daban domin su ƙirga kuɗin.

Sai dai kuma bayan sun kammala lissafi, su ka kira mutanen Tegina, su ka sanar da su cewa babu cikon naira miliyan huɗu da rabi.

“Sai su ka ce sun riƙe Barangana har sai an kai masu cikon kuɗin da su ka nema sannan za su sake shi.

Wani malamin makarantar mai suna Yakubu Idris, shi da wani da aka kama ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa, kafin naira miliyan 30 ɗin da su Barangana su ka kai, can baya sun tattara naira miliyan 25 sun kai, amma ‘yan bindigar ba su saki yaran ba.

“Mun yi imanin cewa kuɗin sun cika cif-cif, kawai dai ‘yan bindigar sun yi ƙaryar cewa kuɗin ba su cika ba, don su ƙara tatsar kuɗi ga iyayen yaran.”

Mai wannan maganar bai bayyana sunan sa ba, ya ce Gwamnatin Jihar Neja ta hana su yin magana da manema Labarai.

Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Ibrahim Matane, ya ce gwamanti ba ta son yin amfani da ƙarfi wajen ƙwato yaran, don kada tsautsayi ya sa a halaka wasu daga cikin su.

Ya ce ana tattaunawa da ‘yan bindigar. “Saboda mun san wajen da ake tsare da su. Mu na kauce wa amfani da sojoji ne don kada a kirkure a kashe yaran.”

Ya ƙara da cewa gwamnati na ƙoƙarin bin wata hanyar sako yaran ba tare da an biya diyya ba

Mahara sun sace yaran tun a ranar 8 Ga Muyu. Wasu iyaye biyu an tabbatar da cewa sun mutu, jin cewa yaran su na cikin waɗanda aka yi garkuwa da su.

Share.

game da Author