AREWA A HANNUN ‘YAN BINDIGA: Waɗanda su ka yi garkuwa da Sarkin Kajuru sun nemi fansar naira miliyan 200

0

Waɗanda su ka yi garkuwa da Sarkin Kajuru a Jihar Kaduna sun nemi a biya su diyyar naira miliyan 200, kafin su sake shi da sauran iyalin sa 12 da su ka tsare.

Majiya mai tushe daga Fadar Sarkin Kajuru ta shaida wa DailyTrust cewa an yi magana da ‘yan bindigar, kuma ana ci gaba da tayawa su kuma ‘yan bindiga na cewa ‘albarka.’

Ɗaya daga cikin masu naɗa Sarki a Kajuru ne ya yi wa jaridar ƙarin bayani.

Yadda Aka Yi Ɓarin-wuta Kafin A Tafi Da Sarkin Kajuru:

Waɗanda jaridar ta tattauna da su, sun ce maharan sun datse duk wata hanyar shiga Kajuru, garin da tafiyar kilomita 37 ce tsakanin sa da Kaduna.

Hajiya Hadiza matar Sarki Alhassan ta shaida cewa ita ce matar sarkin ta biyu.

Ta ce, “bayan sun fasa ƙofa sun shiga gidan, sun tambaye ni inda Sarki ya ke. Na ce masa ba ya nan.

“Daga nan wani ya riƙa yi min ihu sai na faɗi inda Sarki ya ke. Su ka ce idan mu ka shiga mu ka gano shi, za mu gamu da ke.”

Ta ce bayan sun ƙara shiga ciki, su ka fasa ɗaki, su ka fito da shi. Su ka ce kai ne Sarki? Ya ce ni ne Sarki. Daga nan su ka tafi da shi.”

Sauran Iyalan Sarkin Kajuru Da Ke Hannun ‘Yan Bindiga:

Akwai wata ‘yar da Zainab mai shekaru 25. Sai wata jikar sa Zainab Muktar mai shekaru 15.

Akwai kuma jikokin sa maza su huɗu, sai kuma Sallaman Ssrki da wasu ‘yan uwan sa shida.

Cikin bayanin da Gwladiman Kajuru Dahiru Abubakar ya yi wa manema labarai, ya ce sun yi magana da Sarkin, ana kan tattaunawa, kuma ya na cikin ƙoshin lafiya shi da sauran waɗanda aka yi garkuwa da su.

Tuni dai Rundunar ‘Yan Sandan Kaduna ta ce an bazama neman su a duk inda ake tunanin an tsare su.

Wasu rahotanni kuma sun tabbatar da cewa Sarkin ya kira taron ɗaukar matakan tsaro, kwana ɗaya kafin sace shi, inda ya ce akwai ƙishin-ƙishin ɗin ana ƙulla yadda za a yi garkuwa da shi.

PREMIUM TIMES Hausa ta bada labarin cewa an sace Sarki sukutum da iyalan sa 12 a Kaduna.

‘Yan bindiga sun sun yi wa garin Kajuru shigar-kutse, su ka yi gaba da Sarkin Kajuru, Alhassan Adamu.

Sun ritsa basaraken na Karamar Hukumar Kajuru a gidan, su ka yi gaba da shi da kuma iyalan sa 12.

Cikin waɗanda aka sace ɗin har da mata da ƙananan yara.

Jikan Sarki Alasan, wanda kuma shi ne Ɗankajuru, mai suna Sa’idu Musa, ya shaida wa Daily Trust tabbacin garkuwar da aka yi da kakan na sa da kuma iyalan sa.

Ya ce lamarin ya faru kamar wajen 12:30 na Asabar da dare, wayewar yau Lahadi.

Jaridar Daily Trust da ta fara wallafa labarin ba ta samu jin ta bakin Kwamishinan Harkokin Tsaro na Jihar Kaduna ba, Samuel Aruwan.

Haka shi ma Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Kaduna, Jagile Mohammed, bai ɗauki wayar kiran da aka yi masa ba.

Share.

game da Author