Aƙalla fiye da fasinjoji ko matafiya 50 ne wasu riƙaƙƙun ‘yan bindiga su ka tare a hanyar Gusau zuwa Sokoto, da rana a ranar Lahadi.
Ganau ya ce sun tare hanyar ce tsakanin Lambar Tureta da Lambar Bakura, su ka kwashi matafiya, su ka nausa daji da su.
Gwamnatin Jihar Sokoto ta tabbatar da lamarin, amma ba ta bayyana adadin yawan mutanen da aka kwashe ba.
Cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su, akwai fasinjojin motar jigilar fasinja ta gwamnatin jihar Sokoto, wato SPORA.
Janar Manajan Hukumar SPORA, Yahuza Chika ya shaida wa manema labarai cewa an kwashi fasinjojin da ke cikin motar su, amma motar guda ɗaya ce.
Sannan kuma ya tabbatar da cewa fasinjoji biyu sun sha da kyar da gumin goshi, amma bai bayyana adadin yawan matafiyan da ke cikin motar da kuma yawan waɗanda aka sace.
Wani matafiyi mai suna Isa Mustapha, ya shaida wa PREMIUM TIMES Hausa cewa ya riƙa jin rugugin harbin bindiga, inda ya yi sauri ya ci burki wajen Lambar Bakura.
Sauran waɗanda PREMIUM TIMES ta zanta da su, ciki har da Ahmed Madunaka, ya ce sun ce bayan ƙura ta lafa, sun ƙarasa su ka ga motoci uku a wurin wayam, duk an kwashe mutanen da ke ciki.
“Abin mamaki, tsakanin Lambar Tureta da Lambar Bakura fa akwai shingen tsaro na daban-daban sun kai 10, amma wannan mummunan al’amari ya faru.” Inji Madunaka.
Mahara na ci gaba da cin karen su ba babbaka a jihohin Arewa maso Yammacin Ƙasar nan, a yankunan da babu jami’an tsaro da waɗanda ke da jami’an tsaron.
Ko a ranar Juma’ar da ta gabata mahara sun dira garin Marabar Jos da rana kata, su ka darkaki ofishin DPO na ‘yan sanda, domin kwasar bindigogi da ƙarfin tsiya.