AREWA A HANNUN ƳAN BINDIGA: Ƴan bindiga sun ƙara sace wani Sarki sukutun

0

Makonni uku bayan sace Sarkin Kajuru a Jihar Kaduna, ‘yan bindiga sun ƙara sace wani Basarake a Gandun Sarki.

An sace Babban Basaraken Masarautar ƙasar Jaba mai suna Sarki Kpop Ham a Gandun Sarki da ke Jihar Nassarawa.

An ruwaito arcewa da basaraken a ranar Litinin, duk da dai har zuwa lokacin da PREMIUM TIMES Hausa ke haɗa wannan labarin babu cikakken bayanin yadda abin ya faru da kuma halin da ya ke ciki.

Sarki Ham shi ne Babban Sarki a ƙabilar Jaba cikin Jihar Kaduna.

Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, Muhammed Jalige, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ya na tuntuɓar rundunar ‘yan sandan jihar Nassarawa a kan lamarin.

Sai dai kuma ya ce har yanzu ba su samu wani cikakken bayani daga gare su ba.

Sace Sarkin Jaba ya kasance makonni uku bayan sace Sarkin Alhassan Adamu na Kajuru. Sarakunan biyu dai duk a yankin Kudancin Kaduna su ke, yankin da ke fama da tashe-tashen hankula tsawon shekara da shekaru.

Har ila yau a ranar Litinin PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin kisan wani jigo a jam’iyyar APC wanda ɗan takarar shugaban ƙaramar hukuma ne da aka tsinci gawar sa da safiyar litinin.

Wani Ƴan uwan marigayin da ya tabbatar aukuwar abin ya ce an kashe Cashman tun ranar Alhamis ne amma sai yau litinin aka tsince gawarsa.

Share.

game da Author