Wata Ƙungiya mai suna Gidauniyar Kare Lafiyar da Nagartar Ƙasar Noma (The Health of Mother Earth Foundation), ta shawarci ƙananan manoma su daina amfani da irin shuka ɗan-kamfani (GMO), wanda aka haɗa da sinadarai domin ya yi yawa da girma ko saurin ƙosawa.
Gidauniyar ta bada wannan shawara ce domin a riƙa kare ingancin ƙasa.
Gidauniyar ta yi wannan kira a Abuja a ranar Talata, a wurin wani taron masana magunguna kan irin noma na GMO a Najeriya.
Sun ce maƙasudin kiran shi ne domin a tabbatar cewa irin shuka ɗan-kamfani da ake haɗawa da sinadaran magunguna bai lalata irin shukan gargajiya da kuma ƙasar noma ba.
Sannan kuma sun ce irin shuka na gargajiya shi ne ainihin irin shukar da zai samar da wadataccen abinci a ƙasar nan, ba irin shuka ɗan-kamfani ba.
Gidauniyar ta ce ci gaba da shuka iri ɗan-kamfani zai haifar da ƙarancin abinci da kuma ɓata muhalli da tawaya ga lafiyar jama’a.
An daɗe ana ce-ce-ku-ce a ƙasar nan dangane da abin da wasu ke gani cewa irin shuka ɗan-kamfani ya na da illa a ƙasar nan. Yayin da wasu ke ganin alfanun sa, wasu kuma da dama na duban illar sa ta fi alfanun sa yawa.
Masana da masu bincike da dama sun haƙƙaƙe cewa irin shuka ɗan-kamfani na haifar da illa ga ƙasar noma, ga sauran shuke-shuke da ‘ya’yan itatuwa da kuma kashe ƙwayoyin halittun cikin ƙarƙashin ƙasa.
Da ya ke jawabi, Daraktan Gidauniyar HOMEF a Najeriya, Nnimmo Bassey ya ce sai ‘yan Najeriya sun yi riƙo da amfani da irin shukar su da irin ‘ya’yan itatuwan su na gargajiya sannan za a iya samun wadatar abinci a ƙasar nan.
Discussion about this post