An sake yin garkuwa da daliban makaranta a Kaduna da safiyar litinin

0

Mahara sun sake yin garkuwa da daliban makarantar sakandaren ‘Bethel’ dake Maramara a karamar hukumar Chikun jihar Kaduna.

Maharan sun afka wa makarantar da safiyan Litinin suna harbi ta ko ina.

Zuwa yanzu ba a san yawan yaran makarantan da suka sace ba.

Wannan shine karo na huɗu da mahara ke yin garkuwa da daliban makaranta a jihar Kaduna a tsakanin watannin shida.

Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda mahara suka afka kwalejin kimkiya da fasaha Nuhu Bamalli da ke Zariya suka arce da ɗalibai da wasu malamai.

Wani da ga cikin daliban da aka harba da bindiga mai suna Ahmad ya rasu awowi bayan an kwantar dashi a asibiti sannan
Har yanzu daliban na nan tsare wajen ƴan bindigan

Yin garkuwa da mutane a jihar Kaduna ya yayi tsanani a ƴan kwanakinnan domin ko ranar Lahadi wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da jarirai, nas-nas da jami’an tsaro a cibiyar kula da masu cutar kuturta da tarin fuka dake Saye a Zariya.

Maharan sace mutanen ne bayan sun yi musayar wuta da ƴan sandan Saye.
Rundunar ‘yan sanda ta ce ‘yan bindigar sun fito ne daga Dajin Sabon Birni da Mulu, kuma a cikin dajin su ka yi garkuwa da waɗanda su ka kama ɗin.

Share.

game da Author