An damke matar Nura Murnai, Ƙasurgumin ɗan bindiga a Katsina da naira miliyan 2 a jakan ta

0

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina Gambo Isah ya bayyana yadda jami’an ƴan sanda suka damke matar wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi wa jihar.

Isah ya ce an kama matar Murnai a bisa babur bayan ta dawo daga Kaduna inda ta je harkar karbar kuɗin fansa.

” An kama mai ɗakin Nura Murnai bayan ta dawo daga Kaduna wajen amsar sakon miliyan biyu daga wurin wani abokin harkar mijin ta, Nura Murnai.

” Da aka bincike ta an samu naira miliyan 2 a cikin jakan ta.

Isah ya kara da cewa iata da kanta ta tabbatar wa ƴan sanda cewa ta na yinwa majinta zirga-zirgar amsar kuɗaɗe daga wurare.

Nura Murnai ya shahara wajen satar mutane da harkallar bindigogi wanda ake nema ruwa a jallo.

Share.

game da Author