Hukumar dake sauraron kararrakin cin zarafi da fyade a jihar Legas DSVRT ta bayyana cewa mata sun ci zarafin maza 194 a watanni shida da suka wuce a sassa da ban da ban a jihar.
Hukumar ta fara daukan rahoton daga watan Janairu zuwa Yuni 2021 sannan ta gabatar da rahoton a cikin makon da ta gabata.
Bisa ga rahoton kashi 44.33% na maza ne suka kawo karar matansu ko wasu matan da ban sun ci zarafin su daga watan Janairu zuwa Yuni 2021.
Sannan daga watan Janairu zuwa Yuni 2020 hukumar ta saurari kararrakin cin zarafi daga maza 108 a jihar.
Hakan ya nuna cewa mata sun fi cin zarafin maza a cikin wannan shekara.
Bayan haka DSVRT ta saurari kararraki 1329 wanda daga ciki mata 1,125 da maza 194.
Daga cikin wannan yawa akwai ma’aurata wanda suka kai 77%, wadanda ba su da aure kuma sun kai kashi 11%, kashi 7% kuma zaurawa ne sannan kashi 5% marasa aure amma suna zaune da samarin su kamar ma’aurata.
Daga cikin mutum 1,329 din akwai mutum 1,236 dake da shekaru 18 zuwa 45 sannan da mutum 93 masu shekaru 45 zuwa sama.
Kodinatan DSVRT Titilola Vivour-Adeniyi ta bayyana cewa tun a shekaran 2014 hukumar take sauraron kararrakin cin zarafi daga mata da mazan jihar.
“Abin kunya ne ga namiji idan har ya shigar da kara cewa mace koda ba matarsa bane ta ci zarafin sa. A dalilin haka maza suke kin yin magana koda mace ta ci zarafin su.
“Idan aka wayar da kan maza kan mahimmancin kawo kara idan an ci zarafin su kamar yadda ake yi wa mata zai taimaka wajen kawo karshen wannan matsala.
Discussion about this post