A hira da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi da Tashar RFI wanda suka saka a shafin su ranar Juma’a, Lamiɗo ya ce mutane ne ba su gane ba, ” Shi Buhari na yi wa Najeriya ganin ganima ce fa da ya samu bayan nasara a yaki da yayi na samun ƴan Najeriya su zaɓe shi tun a 2015″.
Tsohon gwamna Lamiɗo ya kara da cewa tunanin Buhari gaba ɗaya irin na Soja domin dama shi tsohon Soja ne, saboda haka shi fa a ganin sa ganima ce Najeriya wanda yayi nasara akai.
Saboda haka zai yi yadda yaga dama tunda shi a ganisa shine mai mallakin Najeriya sukutum ɗin ta matsayar ganimar sa.
Da aka tambaye shi game da ɓarakar da ke cikin jam’Iyyar sa ta PDP, Lamiɗo ya ce ko da rikici a PDP ko babu, PDP ce za ta kafa gwamnati a 2023.
” Ina so in gaya muku cewa, ko PDP tana cikin ruɗani, ko bata cikin ruɗani, 2023, ita zata kafa gwamnati. Ina so ka rubuta haka ka ajiye.
Sannan ya kuma ce idan ba don kujera ta siyasa ba wani gwamnan Yobe, Mala Buni ko Kuma wai Yahaya Bello me za su ce yayi tasiri a kasa. Kujera ce ke magana ba wai su ba.
Shekarar 2023 dai sai daɗa karatowa ta ke yi sannan kuma ƴan siyasa sai wasa wukaken su suke yi domin runkarar ta.