Ɗan haya ya maka mai gida a Kotu kan bacewar kuɗin sa har Dala 5000 a lokacin da yake korar sa daga gidan da karfin tsiya

0

Christian Emekakwe dake haya a gidan Remilekun Omosehin ya kai kara kotun majistare a Legas, yana neman kotu ta bi masa hakkin sa sannan ta tilasta wa mai gidan hayan sa ya biya shi kudin sa da suka bace a lokacin da yake fatattakar sa daga gidan.

Kotun ta gurfanar da Omosehin mai shekara 53 ranar Juma’a bisa laiffukan koran mai haya daga gidansa ba tare da izinin kotu ba, lalata kayan mai haya da sata.

Omosehin ya musanta aikata laifukan a kotu.

Lauyar da ta shigar da karar Rita Momah, ta bayyana wa Alkali cewa Omosehin ya kori Christian ranar 26 ga Yuli da misalin karfe 6:30 daga gidan da yake haya dake Lamba 73 layin Ayedun a Bariga.

“Christian ya yi asaran wasu kayan sa sannan kudin sa har dala 5,000 sun bace a dalilin fitar da shi ta karfin tsiya da Omosehin ya yi.

Ta ce hakan da Omosehin ya yi ya sabawa dokar jihar Legas na shekaran 2015 sashen 168, 287, 339 da 411.

Alkalin kotun Adeola Adedayo ya bada belin Omosehin akan Naira 300,000 tare da gabatar da shaidu biyu.

Adedayo ya ce za a ci gaba da Shari’a ranar 17 ga Agusta.

Rikici tsakanin masu gidan haya da wadanda ke zaman gidan haya rikici ne da ya daɗe yana faruwa.

A lokutta da dama akan samu rashin jituwa tsakanin masu gidajen haya da masu zaman gida haya idan lokacin biya yayi shi kuma ɗan haya bashi da kuɗin biya, sannan kuma mai gida ya matsa dole sai an yi.

Ko kuma shi kansa mai gidan haya ya rika kara kudin haya na babu gaira babu dalili, sannan kuma da ƙazanta.

Irei-iren waɗannan rashin jituwa daɗaɗɗen abu ba sabo sai dai kuma abin ya kan kazanta da har sai an garzaya kotu idan aka gaza samun daidaituwa.

Share.

game da Author