Gwamnatin Najeriya ta bayyana shirin ko-ta-kwanan ɓarkewar sabuwar zazzafar cutar korona samfur ta uku, mai suna ‘Delta’ a jihohin Kano, Lagos, Ribas, Oyo, Kaduna da Filato da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
Wata sanarwa da Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Daƙile korona, Boss Mustapha, ta ce “kwanan nan ana yawan samun ɓulla da fantsamar launin korona mai zafin nan da ake kira “Delta”.
Mustapha wanda shi ne Sakataren Gwamnatin Tarayya, ya gargaɗi jama’ar ƙasar nan kada su yi wasa ko sakaci, domin ita wannan samfur ɗin ‘korona Delta’, lahira kusa ce.
An kuma umarci dukkan jihohi su gaggauta shiri da kimtsin ɗaukar ƙwararan matakai, fiye ma da wanda aka ɗauka a farkon ɓarkewar korona.
A Yi Kaffa-kaffa Da Ɗaukar Cutar Korona A Masallatan Idi -Inji Gwamnatin Tarayya
Daga cikin matakan kariyar da Gwamnatin Tarayya ta ce jama’a su ɗauka, akwai yin Kaffa-kaffa da kuma hana shiga tirmitsitsin jama’a a masallacin Idin Babbar Sallah da za a gudanar ranar Talata mai zuwa.
Jama’a Su Karkasu A Yi Idi A Filayen Harabar Masallatan Juma’a:
Kwamitin Korona ya ce masallata su karkasu maimakon a cunkushe a masallaci ɗaya, a barbazu masallatan Juma’a kai waye.
“Kwamiti na taya dukkan Musulmin ƙasar nan murnar Babbar Sallah. Sai dai kuma ya na jan hankalin Gwamnatocin Jihohi da limamai su faɗakar kan ɓarkewar sabuwar cutar korona, wadda ta fi biyu na baya saurin illata wanda ta kama.
“A rarrabu a yi Sallar Ido a wurare daban-daban, har a cikin unguwanni, ba sai an ɗunguma kowa ya je filin Idi ba. Sannan kuma a daina haɗuwa a cikin ɗaki jama’a na cunkushewa.”
A Taƙaita Hawan Sallah: Kwamiti ya ce a taƙaita yawan sallah da ake yin cinkoson kallon sukuwar dawakai ko hawan sarakai a biranen Arewacin ƙasar, inda ake shafe kwanaki ana ruguntsimin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe.
Waɗannan bukukuwa ma kwamiti ya ce wurare ne na yaɗa cutar koron.
Kwamiti ya ja hankalin Jami’an Hula da Shige da Fice a kan iyakokin ƙasar nan cewa su tsaurara tsaro kada aka riƙa kwararowa cikin ƙasar nan ta hanyoyin mota da ruwa da jiragen sama.
Korona: An Kulle Lambunan Shaƙatawa da Gidajen Holewa a Abuja
Kwamitin ya ce ya bayar da umarnin ɗaukar matakai a Abuja tun kafin bukukuwan Sallah a gaggauta kulle duk wani lambun da ake shaƙatawa ko holewa a cikin sa a lokutan bukukuwan Sallah.
Sakataren Yaɗa Labarai na Ministan Abuja, Anthony Ogunleye ne ya bada sanarwar kulle dukkan wuraren shaƙatawar a ranar Asabar.
:
1. Tilas a kai wadattattun ruwan sabulu da bokitan wanke hannaye a ƙofar shiga da ta fita masallatan Idi na Abuja.
2. Limamai su tabbatar sun taƙaita huɗuba.
3. Kada a wuce awa ɗaya a Sallar Idi.
4. A tabbatar ƙofodin shiga daban, na fita ma daban. Wato kada a yi turereniya.
5. Duk mai sallah ya je Masallacin Idi da takunkumin rufe baki da hanci.
6. A ci gaba da yawaita wanke hannu, kuma a daina shiga cinkoso ko naniƙe juna.”