Ƴan sanda sun kama direban dake haɗa baki da ƴan fashi suna yi wa mutane sata a Jigawa

0

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta kama wani direban motar haya dake haɗa baki da ƴan fashi da makami suna yi wa fasinjoji sata a jihar.

Kakakin rundunar Lawan Adam ya ce an kama Yahaya Muhammad ranar 20 ga Yuli da misalin karfe 11:30 na dare bayan fasinjojin da ya ɗauko sun kawo kara a ofishin ƴan sanda.

Muhammad mai shekaru 28 mazaunin kauyen Kangire ne dake karamar hukumar Birnin Kudu kuma yana tuka mota kirar ‘Peugeot Citreon 897 bus’ mai lamba 572 TRN.

Adam ya ce a wannan rana bayan Muhammad ya ɗauko fasinjojin a motar sa sai ya tsaya daukar wani fasinja da za shi kauyen Sara dake karamar hukumar Gwaram a Tsamiyar Tannaga dake iyakar jihohin Kano da Jigawa.

Tsamiyar Tannaga wuri ne da ya yi kaurin suna wajen hare-haren ‘ƴan fashi.

“Da fasinjojin motan su ka ga a wannannwuri ne direban zai dauki fasinja sai suka roke shi kada ya tsaya a wannan wuri gudun kada ƴan fashi da makami.

“Shi kuwa Mohammad a Tsamiyar Tannaga ya taka burki inda kafin fasinjojin sun ankare wasu Fulani da suka rufe fuskokin su suka fito daga cikin daji suka sace wa mutane kudi har Naira 195,000.

“Fasinjojin sun ce suna zargin Muhammad da haɗin bakinsa ne aka yi musu sata a wannan mota.

Adam ya ce rundunar za ta kai Muhammad kotu bayan ta gama bincike.

Share.

game da Author