Ƴan bindiga sun yi wa hedikwatar ƴan sanda dirar-mikiya, sun jikkata jami’ai uku

0

Rundunar ‘Yan Sanda ta tabbatar da gaskiyar wani hari da ‘yan bindiga su ka kai wa Ofishin DPO na Maraban Jos da ke Kaduna.

Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, Muhammed Jalige, ya ce ‘yan bindigar sun kai harin da rana kata, wajen ƙarfe 11 na safe a ranar Juma’a, da nufin satar bindigogi da albarusai.

Sai dai kuma a cewar sa, jami’an tsaron da ke wurin sun fatattaki maharan, ba su bari an saci makaman ba.

“Yan bindiga sun yi gangamin da su ka ciko mota ƙirar Sharon uku, su ka kai harin da nufin sace makaman da ke hedikwatar ‘yan sandan ta Marabar Jos. Sun riƙa yin harbin kan-mai-tsautsayi da nufin samun damar kutsawa ɓangaren ajiye makamai.” Inji Jalige.

“Sai dai kuma maharan sun kwashi kashin su a hannun zaratan ‘yan sandan da ake wurin.

“An yi gumurzu sosai na tsawon mintina da dama. A ƙarshe tilas da maharan su ka ga an fi ƙarfin su, sai su ka arce, bayan an ji wasu daga cikin raunuka.”

Jalige ya ce ‘yan sandan da ke wurin sun ƙi barin a sace makaman da ke ofishin na su, saboda tsananin kishin ƙasa.

“Sai dai abin baƙin ciki an ji wa wani sufero da kwansitabul rauni, kuma yanzu haka su na asibiti ana yi masu magani.

“Tuni an fara binciken lamarin ta hanyar amfani da wasu kayan da maharan su ka gudu su ka bari.

An ce za a yi bin diddigin da za a gano maharan, ta hanyar gano masu kayan da aka gudu aka bari ɗin.

“A kan haka Kwamishinan ‘Yan Sandan Kaduna ya yi kakkausan gsrgaɗin cewa jami’an sa su rika tabbatar da tsare makamai da killace su ta yadda ko ana ‘ha maza ha mata ba za a iya sace su ba.” Inji Jalige.

Share.

game da Author