Ƴan bindiga sun sako ƴan makarantan Kaduna 28, an mika su ga iyayen su a galabaice

0

Mutanen da suka halarci wajen mika yaran makaranta 28 da yan bindiga suka sako ga Iyayen su sun yi ta sharɓa kuka cikin tausayi a lokacin da ake mika su ga iyayen.

An rika kiran sunayen su ɗaya bayan ɗaya ana mika su ga iyayen su.

A wani bidiyo da muka gani yaran duk sun galabaita, babu sauran ƙarfi a jikin su, iyayen kuma suna ta koke-koke suna rungumar ƴaƴan su.

Har yanzu dai akwai yaran makaranta kusan 100 dake tsare hannun ƴan bindigan.

Idan ba a manta ba akwai wasu biyu da suka arce daga hannun ƴan bindigan bayan an aikesu su yo ice.

PREMIUM TIMES HAUSA ta ruwaito yadda wani manomi ya tsince su a cikin ƙungurmin daji ya mika wa ƴan sanda.

A jihar Neja, har yanzu ana kai ruwa rana tsaganin gwamnati da mahara da suka sace yaran makarantan Islamiya 200 wanda haryanzu ba a sako su ba.

Maganan biyan kudin fansa a jihar Kaduna babu shi kwatata, domin gwamna Nasir El-Rufai na jami’ar jihar ya rantse cewa ko ɗan sa aka sace ba zai biya ko sisi ba.

” Abinda zan yi shine, in kira shi mu yi sallama, Allah ya haɗa mu a Aljanna idan sun kashe shi.

Share.

game da Author