Ƴan bindiga sun kashe wani jigon APC kuma ɗan takara a Kaduna

0

An tsinci gawar Honorabul Cashman Alamkah ranar litinin kwance dauke da harbin bindiga.

Wani ɗan uwan sa wanda ya tabbatar da rasuwar ɗan siyasan ya bayyana cewa mahara sun kashe Cashman tun ranar Alhamis ne amma kuma sai yau litinin.

Ya ce an kasje marigayin a hanyar Keffi zuwa Akwanga ne a wani gari Yelwa.

Wani jigo a jam’iyyar APC Yahaya Farouk ya tabbatar wa PREMIUM TIMES HAUSA da rasuwar marigayin.

Honorabul Cashman ne ɗan takaran shugaban karamar Hukumar Kachia a ƙarƙashin jam’iyar APC wanda za ayi a Kaduna nan ba da daɗewa ba.

Har zuwa yanzu hukumomi basu sanar da karin bayani akai ba.

Share.

game da Author