Yanzu haka dai mazauna ƙauyukan Zamfara da ‘yan bindiga su ka fatattaka sun fara komawa gidajen su, bayan Hadimin Gwamnan Zamfara mai suna Sidi ya tattauna da gogarman masu garkuwa da mutane a Zamfara, wato Turji.
Idan ba a manta ba, yaran Turji sun kama mazauna ƙauyuka da dama a Ƙaramar Hukumar Shinkafi su ka kai wa Turji ya yi garkuwa da su.
Turji ya ce ba zai sake su ba sai jami’an tsaro sun saki mahaifin sa da aka kama tsakanin Kano da Jigawa.
Yayin da aka tattauna da Turji da Hadimin Gwamna Matawalle, gogarman ‘yan bindigar ya ce ya amince mutanen da su ka tsere ɗin su koma gidajen su.
“Amma dai ba zan saki waɗanda na tsare ba, har sai an saki mahaifi na da aka tsare tukunna.
Cikin wani faifan murya da PREMIUM TIMES Hausa ta saurari ganawar ta su, Turji ya ce shi ba shi da matsala da Gwamnatin Zamfara. Domin a cewar sa, garuruwan da ya je ya kamo waɗanda ya tsare ɗin ma ai shi ke gadin su daga wasu ɓarayin da ke neman afka masu.
Ya ce ya na da matsala da wasu Hausawa ne su biyu, saboda sun ga yadda ya ke taimakon mazauna ƙauyuka ya na kare su daga wasu mahara, kuma ya na kwato masu shanun su, sai su ka fara nukura da shi.
Ya ce su ne su ka tona asirin mahaifin sa na Kano, har jami’an tsaro su ka riƙe mahaifin na sa.
Turji wanda ya ce ya fi ‘yan sanda amfana wa mutanen ƙauyukan, ya ƙara da cewa bai ga dalilin da zai sa a je a kama mahaifin sa ba.
“Idan wani abu ne ai da ni ake yi amma ba da mahaifi na ba. Wanda ya ce idan na saci shanu mahaifi na ke tarawa, ƙarya ya ke yi.
Jami’an tsaron da su ka ce mahaifi na wai ya tafi da shanu na jihar Jigawa, ƙarya ce. Ta ina zai wuce da shanu daga Zamfara har Kano har Jigawa?”
PREMIUM TIMES Hausa ta kasa jin ta bakin Kakakin ‘Yan Sandan Zamfara.
Wani jami’in Zamfara kuwa ya ce batun sakin mahaifin Turji kuwa ba a hannun Gwamnatin Zamfara ya ke ba, “kuma shi ma Turji ɗin bai ce a Zamfara aka kama mahaifin na sa ba.
Sannan kuma wata nahiyar PREMIUM TIMES Hausa ta turo hotunan da su ka tabbatar cewa mazauna ƙauyukan waɗanda su ka gudu sun koma ƙauyukan su.
Batun sakin waɗanda ya yi garkuwa da su kuwa, Turji cewa ya yi idan yanzu aka kawo masa mahaifin sa, to zai saki waɗanda ya yi garkuwar da su.
Ya ce shi ma ba don ya na so ya tsare su ba, kuma ba wahala su ke sha ba.
Yayin da PREMIUM TIMES ta buga cewa mutum 50 ake tsare da su a hannun Turji, wasu jaridu sun ce mutanen sun kai 150.